Saturday, 25 November 2017
Wa'azin IZALA a kasashen Turai Da Lokutan Da Zasuyi Wa'azi a ko wace Kasa Kamar Yadda Wannnan Hotunan Ya Nuna

Home Wa'azin IZALA a kasashen Turai Da Lokutan Da Zasuyi Wa'azi a ko wace Kasa Kamar Yadda Wannnan Hotunan Ya Nuna
Ku Tura A Social Media

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Kamar yadda kuma sani Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, tare da Sakataren Izala Na kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, suna kasashen Turai domin gudanar Da'awa a wannan yanki.

A halin yanzu suna Kasar London, daga bisani kuma zasu shiga zuwa kasashen Germany, France, Belgium, Holand, Italy, Spain, da Greece,  domin aiwatar da aikin Da'awa a wadannan kasashe.

Kungiyar Wa'azi ta Izala a Naijeriya tare da kungiyar Wa'azi ta ''Sautus Sunnah dake kasashen Turai ne sukayi Hadin Gwuiwa domin gabatar da wa'azozin. 

Manufar Ziyarar dai itace, Wa'azi zuwa ga 'yan uwa Na wadannan kasashe, musamman ma 'yan Afurka da suke da Zama a can, da kuma saduwa da cibiyoyin ahlu sunnah na kasashen turai (Europe) Kamar kungiyar 'Sautus Sunnah' mai wa'azin musulunci, da Kira a tsaida Sunnah tsantsa, a fatattaki Bidi'ah, wadanda suke da Zama a can, saboda hada karfi da karfe wajen Da'awa.

Kungiyar ta Sautus-Sunnah Sukanyi taro lokaci bayan lokaci a yankin, kuma a wannan karon sun gayyaci kungiyar Izala ta Kasar Naijeriya domin su shiga wadanan kasashe a ci gaba da Wa'azi ba kakkautawa. 

 Allah ya bada sa'ar Da'awa, yasa a samu gagarumar Nasara.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: