Wednesday, 29 November 2017
Sakon murya na wata mutuniyar Taraba na kara sarkakiya kan batun kisan Bilyaminu

Home Sakon murya na wata mutuniyar Taraba na kara sarkakiya kan batun kisan Bilyaminu
Ku Tura A Social Media

- Matar da ke magana a muryar tace ita a jihar Taraba take

- An dai kashe bilyaminu ne a gidansa dda ke Maitama, sai dai matarsa ta musanta kisansa, inda aka ce tsautsayi ne

- Matar ta ce tana da hujjar cewa Marigayin yana soyayyar batsa da surukar tasa ne, abin da wai ya haukata matar tasa ta dauki mummunan matakiSakon murya da ke yawo a Whatsapp ta wayoyin salula, a arewa, na wata mata, ya sake birkita lamari kan batun kisan da aka yi wa Bilyaminu da makami a makon jiya.

A muryar, wata mata ta kare wadda ake zargi, da cewa ai dole ta dauki irin matakin da ta dauka, saboda wai ai sakon text din waya da ta kama a wayar mijn nata, na hirar batsar soyayya ne tsakanin mahaifiyarta da mijinta, wato wai kwartanci suke.


Babu dai wata hujja da matar ta bayar, duk da tayi ikirarin tana da hujjar hakan, inda tayi Allah-Wadai da Allah-Tsine ga wai matan aure masu neman maza a waje.

Ta yi musu kudin goro gaba daya, inda cikin ashariya ta kira mata da karuwai, ta kuma rantse ko ita ce mutum ya neme ta ya zo ya nemi 'yarta to zata hallaka shi murus har lahira.Ya zuwa yanzu dai, babu wanda ya musanta ko ya gasgata wannan babban zargi daga bakin wannan mata da ba'a fadi sunan ta ba. Duk da cewa uwa da 'ya suna gaban kuliya kan zargin laifukan su daban daban.


Alamu dai na nuna cewa wannan batu baya kusa da mutuwa nan kusa, kuma al'ummar arewa sun kasa kunne sai sunji kwakwap, kamar yadda suke mayatar kallon wasannin Hausa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: