Kannywood

Na Rubuta Fim Din ‘Auren Manga ‘ Fiye da Shekara Biyar Wanda Shine Fim Da Yafi Kowane A Wasan Barkwaci NishadiFitaccen daraktan fina-finan Kannywood Falalu A. Dorayi ya ce ya hada fim din “Auren Manga” ne saboda ya bai wa mutane dariya da sanya nishadi a zukatan masu kallo.

A tattaunawarsa da Nasidi Adamu Yahaya, Baba Falalu, kamar yadda aka fi saninsa a Kannywood, ya ce ya gina maudu’in fim din ne domin ya sha bamban da sauran fina-finan barkwanci.

A cewarsa, “Na rubuta fim din “Auren Manga” ne sama da shekara biyar da suka wuce da zummar marigayi Rabilu Musa Dan Ibro ya zama babban jaruminsa, amma sai Allah ya yi masa rasuwa.

“Don haka ne na yi gyare-gyare a cikinsa kuma ni da kaina na zama babban jarumin cikin fim din”.


“Babban abin da yake koyarwa shi ne yadda ake tilasta wa namiji, wato Manga ya fito da matar da zai aura. Ka ga hakan ya bambanta da yadda aka saba.”

Falalu A. Dorayi ya ce mai daukar nauyin shirin Yakub Usman, ya kashe sama da naira miliyan biyu wurin hada fim din.
Fim din ya hada manyan jarumai irinsu Adam A Zango da Hadiza Gabon da Sulaiman Yahaya (Bosho) da Baban Chinedu da kuma Falalu Dorayi

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?