Friday, 10 November 2017
Matashin Da Ya Fallasa Kudaden Gidan Ikoyi Ya Zama Miloniya - Magu

Home Matashin Da Ya Fallasa Kudaden Gidan Ikoyi Ya Zama Miloniya - Magu
Ku Tura A Social Media

Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya tabbatar da cewa matashin da ya fallasa inda aka boye makudan kudaden nan na Dala milyan 43.4 a wani gida da ke yankin Ikoyi a jihar Legas a halin yanzu ya zama Miloniya.

A bisa sabon salon yaki da rashawa, duk wanda ya taimaka aka gano kudaden sata na gwamnati, za a ba shi kashi 2.5 na yawan kudaden. A cewar Shugaban EFCC, a halin yanzu ana ci gaba da ba matashin horo na musamman kan yadda zai sarrafa kudaden saboda bai taba ganin irin wadannan kudade a rayuwarsa ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: