Thursday, 9 November 2017
Kannywood:- Taƙaittacen Tarihin Jaruma Balkisu Shema

Home Kannywood:- Taƙaittacen Tarihin Jaruma Balkisu Shema
Ku Tura A Social Media
Ita ce matashiyar jaruma wadda tauraronta yake haskawa.' Fim din Tabbatacce Al'amari shi ne wanda ya sanya wannan jaruma darewa matsayi na daya daga cikin jarumai mata a kannywood domin ta shiga tsakiyar gogaggu ta nuna gogewarta.

Kasancewar labarin fim din kusan a kanta yake, hakan ya bata damar taka rawarta har da tsalle. Domin mafiya yawan wadanda suka kalli shirin maganar ta kawai suke yi ba ta sauran jaruman ba.

Yar Asalin Jihar KatsinaTa fara karatun firamari a makarantar Isa Kaita College of Education da sekandari a Government Day Secondary School Dutsin-Ma. 

A wata Hira Bilkisu ta shaida cewa tun bayan da tayi fim din farko taso tayi aure domin har ta daina karbar aiki, amma Allah cikin ikonsa bai nufi yin auren ba, duk dai bata sanar da dalilin da ya hana yin auren ba.


Yan mata da samari na fuskantar kalu bale da yawa daga ciki da wajen masana'antar fina-finai a kokarin su na tabbatar da burin su na zama manyan taurari, amma Bilkisu tun bayan tabbataccen Al'amari Ali Nuhu ya saka ta a wani Sallamar so, sai kuma finafinai irinsu Dawood, Ranah da dai sauransu wanda yanzu haka suna hanya basu fito ba,
Ita ce Wadda aka shirya zata fito a cikin fim din Mansoor sai ta makara ba ta zo da wuri ba har aka canja ta da wata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: