Tuesday, 28 November 2017
Ina da takardan da zan bawa Buhari ya bankado Triliyan Uku -inji Abdulrasheed Maina

Home Ina da takardan da zan bawa Buhari ya bankado Triliyan Uku -inji Abdulrasheed Maina
Ku Tura A Social Media

Ina da takardan da zan bawa Buhari ya bankado Triliyan Uku -inji Maina
Tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa na sauya fasalin hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, yace yana da takardun shaidu da shugaba Buhari zai gano fiye da Naira Triliyan Uku (3tr) a cikin watanni 9.

Mista Maina wanda yayi wata kebantacciyar hira da gidan Talbijin na Channels yace ya nemi duk hanyar da zai gana da shugaban kasar amma anki bashi dama.
Maina wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa yanzu haka hukumar EFCC na nemansa ruwa a jallo.

A cikin tattaunawar wacce gidan TV ya haska a daren ranar Litinin Hausa Times ta jiyo Maina yana cewa galibin makusantan shugaba Muhammadu Buhari da suke kewaye dashi ko ya aminta dasu ba masu nufin gaskiya bane kuma basa fadi mashi muhimman abubuwa da ya kamata ya sani a kasarnan.

A cewarsa idan har akwai mai ja da maganarsa to a bashi dama ya gana da shugaban kasar, ‘ni kuma nayi alkawarin sai na bashi bayanai da takardun sirri da zai bankado fiye da triliyan Uku

Share this


Author: verified_user

0 Comments: