Thursday, 30 November 2017
HUKUNCIN SANYA TUFAFIN ARNA A GARURUWANSU:-Daga Dr. Aliyu Muh'd Sani

Home HUKUNCIN SANYA TUFAFIN ARNA A GARURUWANSU:-Daga Dr. Aliyu Muh'd Sani
Ku Tura A Social Media
Lallai abu ne sananne saba wa Kafirai da Mushrikai a abubuwa na rayuwa da suka kebanta da su yana daga cikin Manufofin Shari'ar Muslunci. Shi ya sa aka samu Hadisai masu yawa sun zo suna umurtanmu da saba wa Yahudu da Nasara a siffofinsu na zahiri, na Tufafi da Al'adu da sauran lamura na rayuwa, kuma suka hana mu kamanceceniya da su da kokkoyonsu.

Amma sai dai saba musun yana kasancewa ne a lokacin karfi da izzan Musulmai. Amma duk inda Musulmai suke da rauni to saba musun ba Wajibi ko Mustahabbi ba ne, matukar zai haifar da cutarwa.

Don haka duk lokacin da Musulmai suka kasance a garuruwan Kafirai da kasashensu to babu bukatar su saba musu, don tsoron cutarwa. Kai, kamantuwa da kafiran a siffofinsu na zahiri, kamar Tufafi da Aski da wasu abubuwan na zahiri zai iya zama Wajibi ko Mustahabbi gwargwadon Maslaha ta Shari'a, kamar zuwa Kasar Kafiran don Da'awa da kira zuwa ga Allah.

Shaikhul Islami ya ce: 
لو أن المسلم بدار حرب، أو دار كفر غير حرب؛ لم يكن مأمورا بالمخالفة لهم في الهدي الظاهر، لما عليه في ذلك من الضرر بل قد يستحب للرجل، أو يجب عليه، أن يشاركهم أحيانا في هديهم الظاهر، إذا كان في ذلك مصلحة دينية: من دعوتهم إلى الدين، والاطلاع على باطن أمرهم لإخبار المسلمين بذلك، أو دفع ضررهم عن المسلمين، ونحو ذلك من المقاصد الصالحة.
اقتضاء الصراط المستقيم لمخالفة أصحاب الجحيم (1/ 471)

"Da ace Musulmi yana kasar abokan yaki, ko kasar kafirci ba abokan yaki ba, to ba a umurce shi da saba wa Kafiran a siffofi na zahiri ba, saboda abin da ke cikin haka na samun cutarwa. Kai, zai iya zama Mustahabbi ko Wajibi a kan mutum wani lokacin ya yi tarayya da kafiran a siffofinsu na zahiri (kamar Tufafi, tara gashi ko aski), idan akwai Maslaha ta Addini a cikin hakan, na kiransu zuwa ga Addini, ko leken asirinsu da kawo labari ga Musulmai, ko kawar da wani cutarwa daga Musulmai da makamancin haka na kyawawan Manufofi".

Saboda haka, matukar akwai Maslaha ta Addini to dacewa da kafirai a Tufafinsu a cikin garuruwansu Wajibi ne ko Mustahabbi. In kuma babu Maslahar Addini hakan halal ne. Musamman saboda yadda a yau ake zargin Musulmai Ahlus Sunna da Ta'addanci. Don haka Wajibi ga wanda ya je Turai don yin Da'awa ya sanya Tufafinsu.

Da wannan nake jan hankalin 'Yan uwa Ahlus Sunna, bai kamata muna kutsawa cikin abubuwan da za su kara Ta'assubanci da rabuwar kai a tsakaninmu ba. Sa'annan kuma yana da kyau mu nisanci dukkan abin da zai zubar da Haiba da Kwarjinin Jagororin Da'awar Sunna. Saboda yana daga cikin manyan sabuba na lalacewar al'umma in ta wayi gari ba ta wasu jagorori a lamuransu da take ganin kimarsu da kwarjininsu, a mayar da kowa bai wuce a ci mutuncinsa da hakki ko ba hakki ba. Sai kuma in wata matsala ta kunno kai mu fara lalubensu wajen warware matsalar.

In muka daraja jagororinmu  Da'awa da dukkan Shugabanninmu sai mu samu hadin kai da cigaban rayuwa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: