Labarai

Hotuna: Maza Na Tsayar Da Ni Su Karɓi Lambar Wayata A Maimakon Su Sayi Ruwan Da Nake Talla- Budurwa Mai Tallan ‘Pure Water’



Sana’ar sayar da ruwan leda da a ke kira da ‘Pure Water’ da ruwan roba ‘Bottled Water’ da nau’ikan lemuka a kan tituna ya zama ruwan dare gama duniya sakamakon karbuwa da sana’ar ta samu a matsayin hanyar samun taro da kobo ga masu yinta da kuma taimakawa masu zirga-zirga a ababen hawa da ma a kasa abin jika makoshi a lokacin da bukatar hakan ta kama


Wata zukekiyar budurwa mai sayar da ruwa a Accra babban birnin kasar Ghana ta koka kan yadda maza ke tsayar da ita amma ba don su sayi ruwa ko lemon da ta ke talla ba, a’a, sai kawai don su karbi lambar wayarta da nufin su kirata bayan ta gama tallan don su fahimci juna


Nina Ricchie


Sai dai kuma wannan mai sai da ruwa ba wata bace illa fitacciyar mawakiyar kasar Ghana nan Nina Ricchie ta yi bad da kama a wani salo na yaki da munanan dabi’u a cikin al’umma, musamman ta’adar dora talla ga ‘yan mata



Nina ta dora a shafinta na Instagram yadda ta sha fama da samari a dan fita da ta yi talla na dan sa’o’i kadan, inda ta yi kokarin bayyanawa iyaye irin hadarin da ‘ya’ya mata suke fuskanta a lokacin da suka fita talla



Sau tari ‘yan mata masu talla na karewa ne da tallata kansu a maimakon kayan da suka dauko talla

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button