Wednesday, 29 November 2017
Fim Sana'a ce mai Rufin Ashiri Inji Balkisu Abdullahi

Home Fim Sana'a ce mai Rufin Ashiri Inji Balkisu Abdullahi
Ku Tura A Social Media
Shahararriya kuma matashiyar ‘yar wasan Hausan Kannywood, Bilkisu Abdullahi, tana daya daga cikin jarumai mata da tauraruwarsu ke haskawa a wannan lokacin, a cikin kwanakin nan ta yi finafinai da dama wasu sun fito wasu suna kan hanya.

Bilkisu tana daya daga cikin jarumai mata masu kwazo da maida hankali musamman a ta fuskar masana’antar da kuma ayyukanta. Tana da kwarjini idan aka duba ta fuskar al’umma, cikin kankanin lokaci ta samu karbuwa a idon duniya.

Bilkisu ta na iya bakin kokari ta ga ta birge masu kallo. Akasarin masu kallon fim suna son su ganin ta a ciki finafinai. Jarumar ta kware a gurin rawa da iya magana. Masoya na son ganin ta hau kowace rara da darakta ka iya dora ta.

Al’umma suna yabon Bilkisu kwarai da gaske ta wadannan fuskoki uku musamman gani rawar da ta taka a finafinan ta na kwanan nan.

Bilkisu haifaffiyar garin Legas ce, a nan ta girma a can kuma ta yi Makarantar Noziri da Firamare dinta, daga bisani kuma ta dawo Kano da zama, anan ne kuma ta yi karatun Sakandiri a Dinop International School dake Hotoro, bayan ta kammala karatunta, sai ta shiga harkan fim.

Ta bayyana a Abinda ya ja hankali ta ta fara harkan fim a wata hirar da suka yi da wakilinmu ta ce, “fim akwai abubuwa da dama, fim akwai fadakarwa sosai a cikinsa, ni kaina akwai FINAFINAN da na yi na ga abubuwa sosai wanda ni ma na dau darusa a cikinsa”,
Ta kuma bayyana mana cewa ‘Kanina’ na daya daga cikin finafinan da ita kanta ya birge ta, koda aka tambaye ta dalili, sai tace, “Saboda irin yanda labarin fim din yake, ya yi kyau, kuma akwai darussa a ciki wanda al’umma za su karu da su”.

Ta kuma ba ‘yan uwanta maza da mata na masana’antar Kannyood shawarar da su rike sana’ar fim da hannu biyu, inda take cewa, “Fim dai sana’a ce mai kyau daidai gwargwadon da zaka rufa ma kanka asiri, kuma sannan su yi abinda ya kawo su, sannan su bi ta hanyar da suka san ta alhairi ni, kuma za a taimaka masu kuma mai shi yana da hanyar.”
Koda aka tambayeta wani irin kalubalen ta fuskanta a rayuwarta, da fara harkan fim. Ta ce ita bata fuskanci matsaloli ba gaskiya, sadda ta fara harkan fim, saboda da yardar mahaifanta ta shiga industri, kafin Allah ya musu rasuwa, kuma ko yanzu ba ta wani samun tsangwama daga gurin ‘yan uwanta da masoyanta, suna zaman lafiya har gobe.
Ta bayyana a finafinai da daman Gaske wanda ita da kanta ba za ta iya kawo su ba. Cikin kwanakin nan ta yi finafinai da dama, wadanda al’umma ke sha’awar kallonsu, kamar su Kanina.

Kanina fim ne wanda ya samu ingantaccen aiki da kwararrun ma’aikata, da sabbin fuskan jarumai masu tasowa, da kuma wadanda suka dade a masana’antar, wanda ya hada da irin su: fittaccen jarumi kuma sarkin Kannyood Ali Nuhu, yana cikin fim din kuma shi ya bada umarni, Nazir Dan Hajiya kuma ya dau nauyin shirin, Shamsudden da ita Bilkisu suka fito a matsayin jaruman shirin.

Daga cikin fina-finan da ta yi kwanan nan akwai: Burin Duniya, Kama, Wata Mafita, Nawad, Waye Sila, Nafsi Nafsi, Zan Rayu Da Ke, Zubaidah da dai sauransu.
Fim din Ya A So fim ne da ke cike da ilmantarwa gami da fadakarwa, fim me me dauke da labarin soyayya mai shiga jiki kwarai, tare da kara wayar da kan masoya, wanda ya samu aiki kwararrun daraktoci da furodusosi, dauke kuma da manyan jaruman Hausa fim wadanda suke tashe a wannan lokacin.

Juruman da suka bayyana a wannan fim din ya hada da jarumar Bilkisu, inda ta taka rawar gani kwarai a cikin shirin, sai kuma matashin dan wasan Hausa koma mai hazaka Abdul M. Shareef, ya fito a matsayin jarumin shirin, sun bada mamaki kwarai da gaske ganin yadda suka yi abun da ba a zata ba, don kuwa ba industri kadai ba ko ina ana muradin fitowar shirin.
Sanin kowa ne Bilkisu tana juya alkalami a wannan lokacin, inda ta doke sauran matan da yawan finafinai a shekaran nan.
Ta fara aiki ne a karkashen kungiyar Karami Multimedia, wanda kawo yanzu tana tare da su, akalla jarumar ta kwashe shekaru biyar tana aiki a masana’antar, da kuma fara bayyanar ta a fim a matsayin jaruma yau shekara daya kacal, amma abun dubawa anan shi ne ta karbu matuka a idon al’umma kamar wacce ta dade a na dama furar da ita, dik da cewa ta samu wasu manya jarumai zuwanta Kannywood, hakan bai hana ta nuna ta ta bajintar ba.
Jarumar tana da kyakkyawan mu’amala tare da matashin jarumi Abdul M. Shareef, wanda sun yi finafinai da daman gaske tare, haka zalika kuma sun fi shakuwa da jarumar Nafisa Abdullahi a cikin mata.
Ta kuma baiyana cewa London yana daya daga cikin kasar dake birgeta kuma take sha’awar zuwa. A abinci kuwa tana son cin Indomi, koda aka tambaye ta wani kalan mota ya fi birge k, sai ta ce Honda.
An tambaye ta daga karshe me za ta ce ma masoyanta da masu sha’awar kallon fim din Hausa baki daya, sai ta ce “Nagode kwarai da goyan bayan da suke bani ina kuma masu fatan alheri, Nagode”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: