Wednesday, 8 November 2017
Dubun Wani Saurayi Da Budurwa Da Suka Jima Suna Damfarar 'Yan Kasuwa Milyoyin Kudi A Kano Ta Cika

Home Dubun Wani Saurayi Da Budurwa Da Suka Jima Suna Damfarar 'Yan Kasuwa Milyoyin Kudi A Kano Ta Cika
Ku Tura A Social Media


Dubun wani saurayi da buduruwa ta cika, wadanda suka kware wajen cutar 'yan kasuwa milyoyin kudi a jihar Kano. 

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ce ta cafke wadanda ake zargin masu suna Jessy Isa, dan garin Mubi na Jihar Adamawa tare da buduruwarsa mai suna Jenifer John wacce ta fito daga jihar Bauchi. 

Rundunar 'yan sanda tana bincikar su da laifin fakewa da kasuwanci su yi ciniki da 'yan kasuwa, sannan su karbi kayan milyoyin kudi. Bayan sun gama ciniki ba nan take suke biyan kudin ba, za su nemi da a basu lambar ajiyar kudi ta banki, da sun karba za su tura maka alert na karya da adadin kudinka shaidar sun shiga, kai kuma da ka je bankin domin tabbatar da kudin ka sun shiga sai ka tarar ba wannan kudin. 

Jami‘in hulda da jama‘a na rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya, ya ce dukka mutanen suna tsare a hannun su inda suke fadada bincike kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da su a gaban kotu. 

Daga Ibrahim Rabiu Kurna

Share this


Author: verified_user

0 Comments: