Monday, 20 November 2017
Dan Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Rasu Sakamakon Daba Masa Wuka Da Matarsa Ta Yi A cikin Hotuna

Home Dan Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Rasu Sakamakon Daba Masa Wuka Da Matarsa Ta Yi A cikin Hotuna
Ku Tura A Social Media


Dan gidan tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Bilyaminu Halliru Bello ya gamu da ajalinsa a daren jiya Asabar sakamakon daba masa wuka da matarsa Maryam Sanda ta yi. Bayan ta ci karo da sakon da wata ta turo masa a waya.

Maryam wadda 'ya ce ga tsohuwar shugabar bankin Aso, Hajiya Maimuna, ta dabawa mijin nata wuka har kusan sau uku ne a baya sannan kuma ta yi masa rauni da wukar a mazakutarsa.

Lamarin wanda ya faru a gidan ma'auratan dake Maitama a Abuja, rahotanni sun nuna cewa yanzu haka Maryam tana tsare a sashen binciken manyan laifuka na rundunar 'yan sandan Abuja.
Ga hotunan margayi Bilyaminu da matarsa:-Share this


Author: verified_user

0 Comments: