Sunday, 19 November 2017
Dalilin da ya sa har yanzu ba mu yafewa Rahama Sadau ba – MOPPAN

Home Dalilin da ya sa har yanzu ba mu yafewa Rahama Sadau ba – MOPPAN
Ku Tura A Social Media

Kungiyar masu shirya fina finai ta kasa sashin jihar Kano MOPPAN, ta bayyana hujjar ta na kin yafewa jaruma Rahama Sadau har yanzu duk kuwa da cewa ta aiaka da wasikar ban hakuri bisa laifin da ta aikata da ya kai har ga korar nata.

Sakataren kungiyar, Salisu Mohammed ya bayyana cewa har yanzu basu samu zama sun tattauna akanal’amarin jarumar ba.

A cewar sa laifin da Rahama ta aikata ba karami bane saboda haka bazasyi gaggawan yafe mat aba saboda kawai ta rubuta wasikar neman afuwa.
Wani jami’in kungiyar daban da ba a bayyana suna shi ba ya ce ba lallai ne kungiyar ta yafewa Sadau ba.

A cewar shi “Ta fadi abubuwa da dama, har sai da ta karyata cewa mun dakatar da ita. Ba ni da tabbacin za a bari ta kara dawowa Kannywood”
Ya ci gaba da cewa “Ta sha cewa ita ta ci gaba da rayuwar ta, toh dalilin me ya sa a yanzu ta ke son dawowa? Ba mu son lalataccen kyau daya ya lalata sauran”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: