Monday, 20 November 2017
DA DUMIDUMINSA Shugaba Buhari Ya Fasa Zuwa Kano

Home DA DUMIDUMINSA Shugaba Buhari Ya Fasa Zuwa Kano
Ku Tura A Social Media

Daga Abdulhamid Fansherr Potiskum

Wata kwakkwarar majiya daga makusancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tabbatar wa da jaridar RARIYA cewa Buhari ya fasa zuwa jihar Kano kamar yadda aka shirya a ranar Litinin 27/11/2017.

Zuwan shugaba Buhari jihar Kano abu ne da ke tayar da kura a siyasar jihar Kano. Yayin da wasu ke korafin ya kauracewa jihar Kano da ta fi kowacce jiha ba shi zunzurutun kuri'a gami da yi masa addu'ar samun lafiya. Wasu kuma na hasashen ya kauracewa jihar ne saboda gudun ruruta wutar rikicin da ke tafarfasa tsakanin Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso.

Majiyar ta kara da cewa, ana sa ran sai 6/12/2017 Buhari zai zo. 

Kusan wannan shine karo na biyu da aka daga zuwan shugaban kasar. Domin ko a baya an yayata batun zuwan sa jana'izar amininsa AVM Mukhtar Muhammad.

Ko a jiya Lahadi 19/11/2017 Ganduje ya gayyaci tsohon Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau zuwa asibitocin da ya gina yayin da ya ke mulkin jihar. Wanda kuma sune makasudin ziyarar Buhari jihar Kano domin bude su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: