Friday, 24 November 2017
DA DUMIDUMINSA Atiku Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

Home DA DUMIDUMINSA Atiku Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP
Ku Tura A Social Media

A gobe Asabar ne ake sa ran tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar zai karbi katin zaman sa memba na jam'iyyar PDP a jihar sa ta Adamawa, wanda hakan ke nuni da cewa zai yi bankwana da jam'iyyar APC.

Wata kwakkwarar majiya ta bayyanawa majiyarmu ta Daily Trust cewa Wazirin Adamawan ya kammala shirin ganin ya samu halartar taron PDP na kasa da za a gudanar a ranar 9 ga watan Disamba.

Rahoto daga :- Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: