Saturday, 25 November 2017
Buhari Ya Yabawa Mabiya Darikar Tijjaniyya Kan Zaman Lafiya

Home Buhari Ya Yabawa Mabiya Darikar Tijjaniyya Kan Zaman Lafiya
Ku Tura A Social Media


Shugaba Muhammad Buhari ya yabawa mabiya darikar Tijjaniya kan yadda suke tafiyar da harkokinsu cikin lumana da zaman lafiya inda ya nemi hadin kansu wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da Shugaban Kungiyar Tijjaniya ta Duniya, Sheikh Muhammad Kabir ya ziyarce a fadarsa da ke Abuja inda ya nuna cewa darikar Tijjaniya ba ta da alaka da wata kungiyar ta'addanci sannan kuma tana da sassaucin ra'ayi game da harkokin addini.

Da yake nasa jawabin, Khalifa Muhammad Kabir ya ce su ziyarci Nijeriya don halartar bikin Mauludin wannan shekara inda ya yabawa Shugaba Buhari kan yadda ya samar da hadin kai a tsakanin addinan kasar nan.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: