Wednesday, 22 November 2017
Babu wani dalilin auren mata 4 a Musulunci Inji wata Baiwar Allah Musulma har da ba da dalilan ta

Home Babu wani dalilin auren mata 4 a Musulunci Inji wata Baiwar Allah Musulma har da ba da dalilan ta
Ku Tura A Social Media

- Wata Budurwa dai ta soki maganar kara auren mata

- A cewar ta sam bai dace maza su rika auren mata 4 ba - 

- Sai dai ta jawo ce-ce-ku-ce da wannan kalaman na ta


Mun samu labari cewa wata Budurwa ta jawo ce-ce-ku-ce bayan da ta ce Mata ma su na da bukatar mazajen aure fiye da guda inda tace maza na labewa da wannan su na tsula tsiya.
Labarin ya zo mana bayan da wata Budurwa mai suna Halimah Kumar a shafin ta na Tuwita tace babu wani dalili na auren mata 4 a Musulunci inda ta kafa hujja da cewa da Allah ya tashi Hauwa’u kadai ya halittawa Annabi Adamu. Jama’a dai sun yi mata raddi game da wannan. 

Wannan Budurwa mai suna Halima ta soki yadda wasu matan ke ba maza damar shan wulakanci da sunan zaman aure. Halima Kumar tace idan dai da sha’awa ce dalilin karin aure su ma matan kan su, su na da sha’awar. 

Amma tace ba za ta hana su Mazan aure ba idan sun yi niyya. Halima dai tace su ma mata su na bukatar mazaje hudu-hudu amma daga baya ta nemi tayi togaciya. 

Sai dai da dama sun yi kaca-kaca da ita inda su kace ba ta fahimci addini ba ko kadan.

 Ita dai tace wasu na fakewa ne da wannan su na cin amanar matan su. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: