Saturday, 25 November 2017
Anyi Kira ga Hukumomi da su gaggauta hukunta matar da ta kashe mijinta a Abuja

Home Anyi Kira ga Hukumomi da su gaggauta hukunta matar da ta kashe mijinta a Abuja
Ku Tura A Social Media

Daga Hamisu Nasidi Baban Awwab

Kiran ya fito ne daga Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatissunnah ta tarayyar Naijeriya Shiekh Abdullahi Bala lau a wata tattaunawa ta musamman da yayi da Gidan rediyon BBC Hausa a birnin London.

Sheikh Bala Lau yayi kira ga hukumomi da su Gaggauta Hukunta matar nan mai suna Maryam da ake zargin ta kashe mijinta Bilyaminu in har an sameta da laifin.

Sheikh Lau yace yin hukunci da tabbatar da adalci ne kadai zai kawo karshen irin wannan mummunan lamari a tsakanin mutane.

A nasa bangaren Babban Sakataren kungiyar ta Izala sheikh Kabiru Haruna Gombe ya ja hankalin mata akan suji tsoron Allah  su kuma yarda da hukuncin da Allah Yayi na cewa  Namiji ya Auri mata hudu  in zai iya rikesu bisa ga adalci.

Ya kara da cewa in har  irin wannan mummunan  lamari  ya cigaba da faruwa  toh karshe matan ne zasu fada cikin matsala domin mazaje  zasu dena auren su.  Ita kuma mace Allah yayi tane domin ta jingina sannan ne zata samu rayuwa mai kyau.

Malaman sun kai ziyara kasashen Turai ne domin amsa gayyatar Da'awa domin gudanar Da'awa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: