Tuesday, 28 November 2017
An sauke hotunan Buhari a Kano sakamakon kin zuwansa jihar

Home An sauke hotunan Buhari a Kano sakamakon kin zuwansa jihar
Ku Tura A Social Media
An sauke hotunan Buhari a Kano sakamakon kin zuwansa jihar
Rahotanni daga jihar Kano suna bayyana cewa wasu mafusata sun farwa allunan tallan Shugaba Buhari da Gwamnatin Kano ta sassaka a waje da dama a cikin birnin jihar suna cirewa tare da farfasawa a sakamakon kin zuwa da Shugaban kasar yayi a jiya litinin.

Tun farko dai anyi ta yayata cewa shugaban zai kai ziyarar aiki Kano a ranar Litinin 27 ga watan Nuwamba har takai ga aka rika sanarwa a gidajen Radiyo a jihar ta Kano cewar mutane su fito su yi turururwa domin tarbar Shugaban kasar.

Sai dai daga bisani Hausa Times ta ruwaito Mista Buhari ba zai je Kano a watan Nuwamba ba. Hausa Times ta ruwaito wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa na bayyana cewa ‘dama tun farko Buhari bai ce zai ziyarci Kano ba kawai dai wasu makusantan shugaban ne suka kirkiri zancen suka yada’

Hausa Times ta bayar da labarin cewa ‘anyiwa shugaban kasar riga malam masallaci. Domin a ranar Litinin ma shugaban zai fice daga kasar’ kuma hakan akayi.
Hausa Times ta ruwaito dama cen an tsara mista Buhari zai ziyarci wasu jihohi a Arewacin kasar ne ciki har da jihohin Kano da Katsina a farko-farkon watan Disamba ba Nuwamba ba kamar yadda aka yita yadawa.

Sai dai wasu rahotanni da ba’a tantance ba sun nuna har a gidan Gwamnati an sauke hotunan shugaban kasar a wasu wuraren a yayinda mafusata kuma a waje suka rika cirewa tare da balle allunan dake dauke da mista Buharin da aka kakkafa a cikin gari.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: