Friday, 10 November 2017
A Karshe Buhari Ya Koma Asalin Ofishinsa A Yau Juma'ah

Home A Karshe Buhari Ya Koma Asalin Ofishinsa A Yau Juma'ah
Ku Tura A Social Media

A karshe Shugaba Muhammad Buhari ya koma asalin ofishinsa wanda ya kauracewa tun bayan da ya dawo jinya daga waje kuma ya kama aiki a ranar 19 ga watan Agusta.

An dai jima ana jita jitar cewa, Shugaban bai samu sauki ba tun da aka samu rahotannin cewa daga cikin gidansa yake aiki amma kuma daga baya Kakakin Fadar Shugaban kasar ya yi karin haske kan cewa ana gyaran ofishin ne sakamakon barnar da beraye suka yi. Sai dai kuma wasu majiyoyi sun nuna cewa kauracewa ofishin na da alaka da shawarwarin da aka ba Shugaban kan cewa an dasa wani mugun abu a cikin ofishin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: