Saturday, 25 November 2017
2019: Ba tasirin da Atiku zai yi akan Buhari koda PDP ta bashi takara -inji El-Rufai

Home 2019: Ba tasirin da Atiku zai yi akan Buhari koda PDP ta bashi takara -inji El-Rufai
Ku Tura A Social Media
2019: Ba tasirin da Atiku zai yi akan Buhari koda PDP ta bashi takara -inji El-Rufai
Kasa da sa’o’i 24 da ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar daga jam’iyyar APC Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-rufai ya maida martani.

Majiyar Hausa Times ta ruwaito mista El-Rufai na bayyanawa yan jaridu a fadar shugaban kasa cewa Atiku ba barazana bace ga Buhari koda jam’iyyar PDP ta tsaida shi takara a 2019
Gwamnan wanda ke bayani kadan da fitowarsa daga sallar Juma’a tare da shugaban kasa yace dama tun tuni sun samu labarin Atikun zai fice APC a watan Disamba. Yace gwara ma da ya fice tun kafin ranar

Mista El-Rufai ya kara da cewa dama tsohon mataimakin shugaban kasar dan tsalle-tsalle ne kowa ya sani. Takara ce a ransa

“Amma muna da kyakkywan yakini ko Gwamna daya ba zai bishi ba har Gwamnan jiharsa ta Adamawa Jibrilla Bindo” inji El-Rufai

Share this


Author: verified_user

0 Comments: