Sunday, 1 October 2017
Zahra Buhari Ɗiyar shugaban ƙasa ta nuna facin ran ta game da karancin kayan aiki a asibitin Villa

Home Zahra Buhari Ɗiyar shugaban ƙasa ta nuna facin ran ta game da karancin kayan aiki a asibitin Villa
Ku Tura A Social Media
Ɗiyar shugaban ƙasa Zahra Buhari ta nuna facin ran ta game da yadda allamura ke tafiya a asibitin dake fadar shugaban ƙasa.

Ta tabbatar da rahoton da aka yi a baya na cewa asibitin bata da cikakken kayan aikin da ya kamata.
Zahra ta nuna fushin ta a shafin ta na instagram ranar juma’a 29 ga watan satumba.
Tana neman amsa akan yadda aka kashe naira bilyan 3 daga cikin kasafin kudi da aka ware ma asibitin.
Zahra Buhari tace masu jinya ke siya magunguna, sirinjin allura har ma da safar hannu da kudin su.

Sama da Naira biiyan 3 aka ware ma asibitin fadar shugaban ƙasa kuma ma’aikatan basu da cikakken kayan aiki da zasuyi aiki dashi, menene dalili?
Ina kudin suka shiga? Tunda aka siyo kayan aikin asitin tun farkon shekara ba’a kara siyo wasu ba, menene dalili? Sakatare na dindin muna bukatar amsa”

“ ya za’a ce magani irin parecetamol da su sirinjin hannu har ma da safar hannu babu a asibitin…. Mai yasa masu jinya har da ma’aikatan fadar suna siyan kayayakin da suke bukata da kudin su a asibitin fadar shugaban ƙasa? 


Take tambaya a shafin ta na instagram.
A baya dai kakakin shugaban ƙasa Femi Adeshina yace bai san ko shugaban yana zuwa asibitin Villa domin ganin liƙita.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: