Friday, 20 October 2017
Za’a saki fim Din Abu Hassan A Cikin Wannan Watan

Home Za’a saki fim Din Abu Hassan A Cikin Wannan Watan
Ku Tura A Social Media
Rahotanni sun kawo cewa shahararren fim din nan da mutane ke ta simayin fitowar sa wato Abu Hassan na kan hanya. Za’a kaddamar da wasan a gidan kallo sinima a ranar 27 ga watan Oktoba a jihar Kano. Jarumin da ya dauki nauyin shirya fim din, Zaharaddeen Sani ne ya sanar da hakan ga jaridara Premium Times harma yace tuni sun kammala shirya fim din. A cewar sa zasu fara gabatar da shi a gidan kallon Queen House Sinima dake Ado Bayero Mall dake jihar Kano, sannan daga bisani su haska shi a sauran jihohin kasar. 


Jarumin ya kuma ce a ranar da za’a fara haska fim din, za’a ga jaruman da suka fito a fim din ido da ido. Abu Hassan dai fim ne da ya bada labarin ta’addanci. Zaharaddeen ya ce ya shirya fim din ne domin ya nuna illar wannan abu da irin kalubalen da jami’an tsaro ke fuskanta wajen yakar shi, da kuma yadda iyaye za su kula da ‘yayan su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: