Tuesday, 31 October 2017
Yan Matan Kannywood Ya Zamo Tilas Mu Ceci Kan Mu Da Kan Mu, Inji Wasila Isma'i

Home Yan Matan Kannywood Ya Zamo Tilas Mu Ceci Kan Mu Da Kan Mu, Inji Wasila Isma'i
Ku Tura A Social Media
SHUGABAR kungiyar ’yan fim mata wadanda su ka yi aure, Hajiya Wasila Isma’il, ta bayyana cewa tilas ne matan industiri das u ka yi aure su kula da kan su ta fuskar tarbiyya, su taimaki kan su da kan su, domin kuwa duk abin da ’yan bayan su su ka yi, to zai iya shafar su.
Ta fadi haka ne a wani kwarya-kwaryan taro da kungiyar tasu ta gudanar a Kano kwanan nan.

Sun yi taron ne kamar yadda su ka saba yi a duk shekara, wanda su ka hada shi da shagalin bikin Babbar Sallah. Hakan ya bai wa fitattun jarumai mata da su ka dade ba su ga juna ba damar halartar taron.

Matan sun yi taron a ranar Litinin, 4 ga Satumba, 2017 a wani wajen shakatawa mai suna Green Park da ke Titin Ahmadu Bello a cikin garin Kano.
Tun da farko da ta ke jawabi a wajen, Wasila Isma’il ta bayyana matukar farin cikin ta a game da yadda mata ’yan fim su ka amsa gayyatar su da aka yi. A cewar ta, duk da cewar an yi taro har sau uku a baya, amma babu wani taro da jama'a su ka taru kamar wannan din.
“Haka alama ce da ke nuna manufar mu ta kafa wannan kungiya mai amfani ce, shi ya sa mata su ka amsa gayyatar da mu ka yi masu,” inji ta.

Ta ci gaba da cewa, “A farkon wannan kungiya, mun kafa ta ne don mata ’yan fim da su ka yi aure, ta yadda za mu rinka taimaka wa junan mu, to amma daga baya sai mu ka duba, akwai mata ’yan fim da su ka yi aure kuma auren nasu ya mutu, kuma su na bukatar taimako, don haka ne mu ka buda kungiyar ta zama ta matan aure da su ke gidan mijin su da kuma wadanda auren su ya mutu.

“Don haka ne a wannan taron za ku ga akwai mata da yawa da auren su ya mutu, kuma sun halarci wannan taron. Mun amince mu hadu mu yi tafiya da su, ta haka ne za mu san wadanda su ke da matsaloli kuma mu san hanyar da za mu bi mu tallafa masu, domin mun gano akwai da dama da aka sake su aka bar masu kula da yara.
“Wasu kuma mazajen su ne su ka rasu su ka bar su da yara, don haka akwai bukatar a tallafa masu.

“A yanzu a halin da ake ciki, mu ’yan fim mu na bukatar mu hada kan mu domin mu magance matsalar da ta ke damun matan da su ke cikin harkar fim saboda yadda ake kallon ’yan fim din, domin kada mu rika ganin mun yi aure mun bar harkar, to duk abin da na bayan mu su ka yi to zai shafe mu.
“Kamar maganar da ake yi na cewar ’yan fim ba sa zaman aure, to ni ga ni shekara ta goma sha biyar da aure ina tare da miji na, don haka maganar ’yan fim ba sa zaman aure ba gaskiya ba ne. Mutuwar aure idan ta zo a ko’ina ma ana yi, ba sai ’yan fim ba.”
Daga karshe, Wasila, wadda matar darakta Al-Amin Ciroma ce, ta yi kira ga mata ’yan fim da su ci gaba da kiyaye mutuncin su a duk inda su ka samu kan su.
Ita ma da ta ke jawabi, tsohuwar jaruma Saima Mohammed Raga ta kalubalanci wadanda su ke cewa ’yan fim ’yan iska ne, ta ce wannan ba gaskiya ba ne, domin idan mutum ya so lalacewa ba sai ya shigo harkar fim ba.

“Don haka mu sana’a mu ke yi, ba iskanci ba. Duk da ba za mu ce dukkan mu mutanen kirki ba ne, amma bai kamata a rinka yi mana kudin goro ba,” inji ta.

An dai yi jawabai da dama a wajen, sannan kuma an ware lokacin nishadantar da mahalarta taron inda aka tuna baya wajen saka tsofaffin wakokin finafinan jaruman da su ka hau wakar su na bin ta. Fati Mohammed ita ta hau wakar ‘Sangaya’, Rasheeda Adamu Abdullahi ta hau wakar fim din ‘Sa’a’, kuma duk da yake yanzu ta yi nauyi amma hakan bai hana ta yin rawa da juyi ba; Mansura Isah an saka mata wakar bikin su da Sani Danja.

A karshen taron, an cimma matsayar cewa za a samar da tallafi ga iyalan ’yan fim da su ka rasu, irin su Jamila Haruna, Hajiya Amina Garba (Mama Dumba), da sauran su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: