Thursday, 5 October 2017
'Yan Fim Sun Taimakawa Malam Waragis Daidai Gwargwado,furodusa Inji Usman Mu'azu

Home 'Yan Fim Sun Taimakawa Malam Waragis Daidai Gwargwado,furodusa Inji Usman Mu'azu
Ku Tura A Social Media
Fitaccen furodusan nan na finafinan Hausa, Usman Mu'azu ya bayyana cewa wasu daga cikin 'yan fim sun taimakawa abokin aikin su Malam Waragis wanda yake fama da rashin lafiya.
Usman ya kara da cewa daga cikin 'yan fim din da suka taimaka akwai wadanda na su ya fito fili wasu kuma sun bukaci a sakate sunansu. Ya kara da cewa ba daidai bane a yi wa 'yan fim kudin goro na cewa babu wani daga cikin su da ya taimakawa abokin aikin sana'ar ta su.
"Ba na mancewa ni da kai na akwai jarumar da ta sa na aikawa da mara lafiyan kudi da kayan abinci amma ta nemi a boye sunanta. Baya ga haka 'yan fim irin su Ali Nuhu, Sadik Sani Sadik, Sa'eed Nagudu, Zainab Ziya'u duk sun bada ta gudummawar ga mara lafiyan".

Usman, wanda shi ya shirya finafinai irin su "Bashin Gaba", "Laifin Dadi", "Cikar Buri", "Hedimasta" da sauran su, ya kara da cewa akwai 'yan fim da dama wadanda suka shiga matsalar da ta fi Malam Waragis kuma abokan sana'ar ta su kan taimaka musu.

Usman ya kawo misali da cewa ko a lokacin da tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Fati Suleiman take fama da rashin lafiya 'yan fim ne suka bada gudummawar da aka yi mata aiki a asibiti.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: