Yadda Rayuwa Ta Kasance A Arewa Maso Gabar Kafun Allah Ya Kawo Mana Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Kafun Allah ya mana canji mafi alkairi, Arewa maso gabashin Najeriya mun azabtu a hannun mayakan Boko haram, wasu lokuta kuma a hannun jami'an tsaron ma bamu tsira ba.

A duk lokacin da Boko haram suka kawo hari wani waje (Kasuwa, Tasha, ko Unguwa) to a ranar mutanen dake wannan waje sun shiga uku, bayaga asarar dukiyoyi da rayuka da mutanen wajen suka gamu da ita. Jami'an tsaro sukan biyo baya su gallazawa mutanen dake rayuwa a wajen.

Sau da dama jami'an tsaron sukan shigo waje wajen su kama dukar jama'a tare da tukui kuya wadanda suka kama, wasu lokuta kuma sukan shimfida mutane a rana su tube musu riguna suna bin kansu daya bayan daya, da sunan suna neman mayakan Boko haram.

Ni kaina wani lokaci Allah ne kadai ya kareni daga fadawa cikin irin wannan musubi, a tsohuwar kasuwa dake jihar Gombe, bayan na bar gefen tudun hatsi kenan, sai sojoji sukazo suka kwantarda duk mutunen dake cikin kasuwar.

Mutanen dake yankin Arewa maso gabas mun hadu da balaoi iri iri, amma yanzu cikin yadda da kaddarawar ubangiji abubuwa nata saukakuwa.

Daga Haji Shehu

Share this


0 comments:

Post a Comment