Friday, 6 October 2017
Ya Zama Dole Shugaba Buhari Ya Sake Tsayawa Takara A 2019

Home Ya Zama Dole Shugaba Buhari Ya Sake Tsayawa Takara A 2019
Ku Tura A Social Media
Daga Haji Shehu Kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari (BCO) ta bayyana cewar, 'ya'yan kungiyar suna iya kokarin su ba dare ba rana, domin ganin sun tursasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake neman takara a 2019.
 Shugabannin kungiyar sun tabbatar da cewar suna son Buhari ya sake tsayawa takara ne saboda muhimman nasarorin da ya cimma na kai Nijeriya tudun na tsira, ta fuskokin tsare-tsare, yaki da rashawa da kuma yaki da tarzoma.

 Shugaban Kungiyar Alhaji Danladi Pasali, ya shaidawa manema labaru cewar tsare-tsare kamar su bada lamuni ga manoma (Anchor Borrowers) karkashin babban bankin Nijeriya (CBN) babbar nasara ce. Ya ce, sama da manoma milyan biyu da dubu dari takwas sun amfana da wannan shiri, wasu sun gina gidaje sannan sun je hajji.

 “Yanzu kudaden da muke samu ba daga man fetur bane. Mun ga irin abunda ya faru a hukumar Kwastam, a gwamnatin baya suna shigarwa gwamnatin tarayya naira bilyan 2 zuwa 3, yanzu kuma hukumar tana shigarwa Nijeriya biliyan 36.

 “Mu 'yan Nijeriya, mu muke cewar dole sai Buhari ya sake fitowa takara" Inji Alhaji Danladi Pasali.
Kannywood:-Kalli Hotunan Bukin Auren Sarkin Waka Nazir Ahmad   
Aminu Saira Mai shirya fina-finai Hausa na Kannywood ya samu karuwa 
Kannywood :- Fitattun Fina-finai Hausa 5 da ya kamata ku kalla

Share this


Author: verified_user

0 Comments: