Thursday, 26 October 2017
Wata sabuwa!!! Babban sufeton yan sanda ya baiwa uwargidan shugaban ƙasa motoci biyu - inji Sanata Misau

Home Wata sabuwa!!! Babban sufeton yan sanda ya baiwa uwargidan shugaban ƙasa motoci biyu - inji Sanata Misau
Ku Tura A Social Media
Dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Bauchi Isa Misau ya kara zargin sufeto janar na yan sanda Ibrahim Idris da siyan motoci biyu ma uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari.

Dan majalisar yayi wannan zargin yayin da yake amsa tambayoyi daga kwamitin bincike akan zargin da yayi ma sufeton yan sanda ranar laraba 25 ga wata.

"har yanzu ina da takardar kwangilar da shi IG ya sallamar wa kotu, inda Uwargidan shugaban kasa ta hanyar babban jami'in mai tsaron ta ya bukaci motoci kerar Toyota Hiace da Sienna jeep. A ranar da mai tsaron uwargidan ya rubuta bukatar shine IG ya sa hannu na a bada motocin. wannan baya daga cikin tsari domin idan muka duba yanda tsarin hukumar babu inda aka ce a baiwa matar shugaban kasa motoci biyu" sanatan ya fada ma kwamitin bincike.

Tsohon jami'in hukumar ya kara jaddada cewa ana amfani da alfarma wajen kara mukamin wasu jami'an hukumar domin wasu da basu cancanci samun karin matsayi alhali akwai na gaban su sun samu.
yayi ikirari da sabon mukaddashin kwamishnan yan sanda na jihar Legas Edgal Imohimi ya samun matsayin domin shi abokin gwamnan jihar ne ba tare da an lura cewa akwai wadanda suka fi shi cancanta.

Misau ya kara zargin sufeto Ibrahim Idris da bada kwangilar biliyan biyu (N2 Billion) ga kamfani mai siyar da motocin Peugeot domin samun motoci kerer Toyota.
Bugu da kari sanatan yace an sauya ainihin ranar aje aiki na sufeton yan sanda domin ba haka yake a da baya ba.

Tun ba yau ba sanatan yake zargin Ibrahim da wasu laifuffuka wanda yayi sanadiyar kai karar shi ga kotu daga gwamnatin tarayya inda take zargin shi da cin fuska.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: