Thursday, 12 October 2017
Video:- Sabon jarumi Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya soma fitowa a wasan kwaikwayo (Ga bidiyon)

Home Video:- Sabon jarumi Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya soma fitowa a wasan kwaikwayo (Ga bidiyon)
Ku Tura A Social Media
Shirin “Dele Issues wanda Samuel Ajibola wanda aka fi sani da ‘SPiff’ ke jagoranta zai samu sabon jarumi a sabon shiri ta musamman wanda aka yi wa laƙani da “Dele for President”.

Shirin jerin wasan barkwanci ne kuma a sabon shirin da za’a fitar nan bada jimawa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya haska a ciki.

A cikin sumun-tabin bidiyo wanda aka sako Obasanjo yana goyon bayan jagoran shirin 'Dele' da ya fito takarar shugaban ƙasa.
za'a sako sabon shirin wanda tsohon shugaban kasa ya fito a ciki ranar asabar 14 ga watan octoba 2017.

Wannan shine fitowar shi na farko a cikin shirin wasan kwaikwayo kuma ya nuna basirar sa na yin wasan kwaikwayo a ciki.

Sauran jaruman masana’antar shirya fina-finai sai su zage damtse domin tsohon shugaban ƙasa ya fara fasowa a dandalin

Domin kalla wannan soman tabi sai ku saukar a wayoyinku.

Download video Now

Share this


Author: verified_user

0 Comments: