Sunday, 22 October 2017
Suna Nan Tafe Sabin Fina-finai Hausa Da ke Shirin Fitowa Nan Ba Da Dadewa

Home Suna Nan Tafe Sabin Fina-finai Hausa Da ke Shirin Fitowa Nan Ba Da Dadewa
Ku Tura A Social Media
Masana'antar mai shirya fina-finai hausa na kannywood zata fitar da sabin fina-finai domin nishadantar da jama'a kamar yanda ta saba.
Hakika tunda aka fitar da shirin "MANSOOR", "RARIYA", "KALAN DANGI" da "KUJERAR WUTA" wanda suka mamaye yankuna da dama na fadin kasa masu sharhi na cewa yanayin yanda ake haska fina-finai a masana'antar ya canja salo.

Jerin sabin fina-finai da za'a sako nan ba da jimawa ba daga ganin fostar su muna iya cewa shirin zasu kasance walakin goro a miya ga masoyan harkar fim.
Masoyan fina-finai Hausa ga shiri dake nan tafe wanda nan ba da jimawa ba za'a sako su ga sinima da kasuwa:

M.A.R.I.Y.A

GWASKA RETURN

ABU HASSAN

KANWAR DUBARUDU

HANGEN DALA

KAUYAWA 2017

CIKI DA RAINO

Wasu na cewa lalle Kannywood ta shirya damawa da sauran masana'antu na duniya wajen shirya fina-finai daidai da zamani.
Jaruman tare da masu shiryawa suma sun zage damtse wajen fitar da shiri mai dauke da labari managarci hakazalika salon yadda suke fitar da fina-finai ya canja.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: