Friday, 13 October 2017
Sirikin Shugaba Buhari, Muhammadu Indimi Zai Gina Wa 'Yan Gudun Hijira Gidaje Dari A Borno

Home Sirikin Shugaba Buhari, Muhammadu Indimi Zai Gina Wa 'Yan Gudun Hijira Gidaje Dari A Borno
Ku Tura A Social Media
Daga Adamu Yokom (Dan-Zakeeh)

A yau ne babban dan kasuwan nan na Nijeriya Alh. Muhammadu Indimi ya yi taro a garin Maiduguri. Taron ya samu halartar Gwamna Kashim Shettima, Shehun Borno, Shehun Bama, Shehun Dikwa, da kuma manyan dattawa na garin.

Alh. Muhammadu Indimi ya kaddamar da gudunmawan sa ga 'yan gudun hijrar garin Bama da suka rasa muhallin su, inda zai gina gidaje dari domin ba su karfin gwiwar komawa garin su da zama. Haka kuma za a wadata su da ruwa da kuma abubuwan more rayuwa don jin dadin su.

Muna Addu'a Allah ya saka da alheri, Allah ya karawa Nijeriya zaman lafiya.Share this


Author: verified_user

0 Comments: