Saturday, 7 October 2017
Sarikin Musulmi a Najeriya Yana Taimakon Kafirta Musulmi- inji Shehin malami Dahiru Usman Bauchi

Home Sarikin Musulmi a Najeriya Yana Taimakon Kafirta Musulmi- inji Shehin malami Dahiru Usman Bauchi
Ku Tura A Social Media

IDAN SARKIN MUSULMI YANA SON TAIMAKON AL'UMMAR MUSULMI NE TO DOLE NE A KOMAI YA SANYA TARIKA DA Shi'a A CIKIN DON ZAMAN LAFIYA. AMMA TAIMAKA WA IZALA WAHABIYANCI SALAFANCI DA YAKE SON KASHE MUSULMI DA KAFIRTA SU DA RUSA HADIN KANSU YANA NUNA CEWA SARKIN MUSULMI YANA CIKIN MASU KAFA ASASIN DA ZAI FI BOKO HARAM HATSARI A NAN GABA A NIGERIA.

 Fitaccen Malamin 'Darikar Tijjaniyar nan Shehu Dahiru Usman Bauchi, ya Soki lamarin Marigayi Sheikh Usman 'Dan Fodiyo da Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubaka III. Inda ya fara ta kan Sarkin musulmi da cewa Yanemi gomnoni, ya nemi sarakuna, yanemi masu kudin kasannan su taru su taimaki IZALA zasu kafa mata Hqrt a Abuja, a tara kudi naira million dubu da dari biyar, (N 1005,000,000.00) abunda wani sarkin musulmi bai tabayiba, bayan ubansama yananan aka kafa IZALA, sannan bayan ubansa dasuki yananan a kafa IZALA, bayan dasuki usman cilo yananan yayi zamani da IZALA, amma dukkansu ba wanda yataba cewa sai taimaki IZALA.

 Haka zalika wannan asabar data wuce da juma’a, yayi taro da mutanen kasa wadanda ya gayyata, wai yanzu an kafa majalisa amma wai shine shugabanta, sannan mugun nanan tsohon dan IZALA, Dr. Salisu Shehu wanda shine sakatarensa, wai shine sakatarensa, kuma wai taron zaa hada kan dukkan musulmi wai kowa ya yarda da musuluncinsa, aa, sai dai in Ahmadiyyane yamutu, amma dukkan musulmi ataru a zama abu daya, da kadiriyya, tijjaniya, da IZALA, shi’a da kowace kungiya ta musulunci a hadu, a daina kyamar juna, a daina kafirta juna, kafirta juna kam, ina shine wani yacema kafiri, kaima kace masa kafiri ko? Shine kafirta juna ko? Ai mu bama kafirta mutane, bama kafirta muslmi, sune suke kafirta musulmi, kungiyar da yakewa shugabanci, saboda haka wannan al alamari da yasa a gaba ya shirya dashi da gomnan sokoto, da wadansu zasu gayyato shuwagabanni IZALA na duniya, wato wahabiyoyin jami'oi na duniya wato na Madina, za'a zo ayi babban taro a sokoto a nadashi wato shine shugaban IZALA da sunan wai “RABIDA”
 To motsinsa yayi yawa, muna gayawa dukkan dan tijjaniya bama cikin wannan hadin kai, dukkan dan tijjaniya baya cikin wannan tsari, bazamu bar shehu tijjani mu kama, yama sunansa? Abubkar sani! Ko Sa’ad Abubakar? Bazamu yardaba, shi ba, ba shugabanmu bane.


 Shi ba shugaban mu bane, shugaban Izalane, “Sarkin Musulmin IZALA” Sabo da haka mu bama tare dashi, ba wani jagoranci da yayi, da zaiyi har ya hadamu da izala mubishi, saboda haka wannan shine sabon labarin da muke ciki, yananan yana tararraki, yauma sunyi taro a Katsina, yana girke, irin wannan girkin, a zo za'a kafa majalisar IZALA mai sunan “RABIDA” yazama shine shugabanta kuma sakatarensa Dr. Salisu. Wannan shine abunda ke gabanmu, ina gayamana dukkanmu baruwanmu da wannan hadin kai, baruwanmu, da dukkan abubuwan da zai zamo jagoran IZALA da sunan Sarkin musulmi ba ruwanmu dashi, shi IZALA dai mukuma idan gwamnati tanaso ta mayar mana da dasuki ko ta zabo daga cikin gidan ta nada mana sarkin musulmi, amma fa wannan kam na IZALA NE. Bala'in da wannan kungiya ta jawo mana a NIGERIA bamu fita ba, sai ansake dakko sabon wani abu wanda zai rikita kasa? Saboda haka mudai bamu ciki wannan hadin kai na shugabancin IZALA, kamata yayi ya mata waazi (IZALA) tadawo wajenmu inda tabarmu, kuma mune za’a tura muje mubi IZALA? Musameta can inda take wajen kafurta musulmi da zagin waliyyai? Ba ruwanmu da IZALA, Ba ruwanmu da jagoran IZALA, Allah ya kiyayemu, Alla yagamamu.

ku gaya musu mufa kalifofin shehu Ibrahin ne, kuma a cikin malamai na kasan nan, akwai ma jikan Annabi muhammadu (SAW), saboda haka idan jikan Annabi na wuri ko jahiline, jikan dan Fodiyo malami ya jadashi? balle jikan dan Fodiyon ma jahili, jikan Annabi Muhammadunne malami, idan da kunya da ladabi ai baza ayi hakaba, kana jikan dan Fodiyo, ga jikan Annabi malami, kaja mutane kace zaka kaisu gurin halaka, wurin tashin hankali? Bazamu yarda ba, domin mu tsarinmu na addini bana siyasabene, kuma babu wanda ya isa yasamu cikin siyasa mu yarda, da shi.

 tajjididin shehu dan Fodiyo aikinsa na tajididin addini ya zo Potiskum daga Sokoto? To ko Zuru bai kaiba, akwai wani sarkin musulmi da aka tabayi, wani ritiy gomna yaginawani masallacin jumaa a kusa da zuru, to sai wancan sarkin musulmi suka daidaita akan cewa a baiwa ‘yan IZALA masallacin, da ya aika yagaya masa cewa wasu jama’ar garinku muslmi sunzo sunce in rokeka kabasu masallaci, sai yace kazoo ka yakeni ka bawa musulmi naka masallacin, ko kakan ka dan Fodiyo bai yaki garinmu ba. Nan zurufa! jaddadawar sa yakai kasar cikin yarbawa? Bai kaiba to mu shehu Ibrahim yahada duk duniya gaba daya, bazamu yarda mu a zamto karkashin dan IZALA ya shugabancemu wai shine shugabanmuba. Ku kasance da mu zamu kawo muku na gaba kadan.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: