Tuesday, 3 October 2017
Rashida Mai Sa'a Ta Zama Darakta Na Gidauniyar Atiku Shiyyar Arewa Maso Yamma

Home Rashida Mai Sa'a Ta Zama Darakta Na Gidauniyar Atiku Shiyyar Arewa Maso Yamma
Ku Tura A Social Media
Jarumar finafinan Hausa kuma mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin mata, Hajiya Rashida Adamu Abdullahi wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa'a, ta zama daraktar gidauniyar Atiku Abubakar shiyyar Arewa maso Yamma.

A yayin jin ta bakin Hajiya Rashida kan wannan mataayi da aka ba ta, ta nuna farin cikin ta tare da fatan Allah ya taya ta riko.

Jarumar ta finafinai Hausa, a yanzu haka tana rike da manyan mukamai a kungiyoyi daban-daban.

Ita ce shugabar Gidauniyar Mai Sa'a, mataimakiyar sakataren kungiyar masu shirya finafinan Hausa, shugabar mata na kungiyar matasan jam'iyyar APC da sauransu da dama.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: