Tuesday, 10 October 2017
Nnamdi Kanu Ya Yi Amfani Da Jinyar Mijina Wajen Cin Karensa Ba Babbaka - Aisha Buhari

Home Nnamdi Kanu Ya Yi Amfani Da Jinyar Mijina Wajen Cin Karensa Ba Babbaka - Aisha Buhari
Ku Tura A Social Media

* Abin Kunya Ne A Ce Babu Magani A  Asibitin Fadar Shugaban Kasa

Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa Shugaban Kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da magoya bayansa sun rika cin karensa ba babbaka ne saboda sun ga cewa Shugaban Kasa, Buhari ba ya Nijeriya yana can Ingila yana jinya.

Ta kara da cewa jinyar da Buhari ya yi a Ingila ya kawo tsaiko ga al'amurra da dama a Nijeriya wanda ya ba Nnamdi Kanu damar neman magoya baya a bisa akidarsa ta neman kafa kasar Biyafara.

Haka ma, Uwargidan Shugaban kasar ta caccaki Shugaban Asibitin da ke cikin Fadar Shugaban Kasa, Husaini Manir inda ta ce, akwai lokacin da ta yi fama da rashin lafiya amma aka kasa duba ta a asibitin sai da ta ziyarci wani asibiti mallakar wasu 'yan kasar waje.

Ta ci gaba da cewa dole a binciki kudaden da ake warewa asibitin inda ta nuna cewa mahukuntan asibitin sun mayar da hankali wajen yin sabbin gine gine alhali babu magani a asibitin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: