Wednesday, 11 October 2017
'Yan Nijeriya Sun Yi Zarra A Gasar Masabukar Kur'ani Ta Duniya

Home 'Yan Nijeriya Sun Yi Zarra A Gasar Masabukar Kur'ani Ta Duniya
Ku Tura A Social Media
Taya Murna gar emu 'yan Nijeriya bisa samun gagarumar nasara a Musabakar karatun Qur'ani Mai Girma ta duniya da aka kammala yau a Birnin Makkah ta Saudi Arabia.

1-Faisal Muhammad Auwal daga Jihar Zamfara ya wakilci Nijeriya a matakin Hizif 60 da Tafseer kuma ya yi nasarar zamowa na biyu a Duniya.


2- Albashir Goni Usman daga Jihar Borno ya wakilci Nijeriya a matakin Hizif 60 kuma ya yi nasarar zamowa na biyu a Duniya.

Ba shakka wannan ba karamar nasara ba ce ga Nijeriya kuma irin wannan nasarar ce ya kamata mu nuna farin cikinmu da ita.

Sannan muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Karrama wadannan Yaran da suka nuna Hazaqa tare da samowa Nijeriya Wannan gagarumar nasarar.
ALLAH ya sanya Albarka."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: