Wednesday, 11 October 2017
'Yan Nigeria sun yi dirar mikiya kan matar da Buhari ya ba mukami

Home 'Yan Nigeria sun yi dirar mikiya kan matar da Buhari ya ba mukami
Ku Tura A Social Media
Nada wata Musulma a mukamin mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya ya tayar da muhawara a kasar, bayan da wasu Musulmi masu tsattsauran ra'ayi daga yankinta na arewacin kasar suka zarge ta da sanya tufafi mai nuna jiki - amma wasu kuma sun kare ta.
Aisha Ahmad, wata babbar ma'aikaciya ce a Diamond Bank, daya daga cikin manyan bankunan Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ke son nada ta domin ta maye gurbin Sarah Alade, mataimakiyar gwamnan babban bankin kasar wadda ta yi murabus bayan ta shafe shakara 23 a kan aiki.

Misis Ahmad, mai shekara 40, 'yar asalin jihar Neja da ke arewacin Najeriya ce, yankin da mata ba sa yawan samun ilimi idan aka kwatanta da kuduncin kasar, kuma wuri ne da damarmaki ga mata a kasuwanci ka iya yin kadan.
Duk da haka, rahotanni daga Najeriyar sun ce ta yi karatun digiri daban-daban, ciki har da wanda ta yi a Cranfield School of Management da ke Birtaniya, kuma ta yi aiki a manyan bankuna daban-daban.

Jim kadan bayan sanar da nadin da aka yi mata, sai tattaunawar ta sauya daga zurfin Karatu zuwa ga yanayin suturarta.
Hotunan da aka dauka daga shafukanta na sada zumunta sun janyo suka daga masu ra'ayin rikau na addini daga arewacin Najeriya.
Wasu malamai, wadanda suke da mabiya sosai a intanet sun ja ayoyi daga Al-Qur'ani, kuma sun hakikance cewar dole mata su suturta jikinsu da kyau kamar yadda addini ya tsara - inda suka soki hotunanta da ke ta yawo a shafukan sada zumunta wadanda ba ta rufe kanta ba.


Wani mutum da ya soke ta, Abubakar Almajiri, ya siffanta Misis Ahmed a matsayin "karuwa" a shafinsa na Facebook kuma ya ce nadinta "rashin adalci ne ga Musulmai."
Almajiri ya yi tir da Shugaba Buhari, yana mai cewa: "Muna tsammanin idan bai zabi iri mai kyau daga cikinmu ba, to ya zabi Musulmi mai dan girmama addini a wannan matsayin."
Da alama yawancin wadanda suka soki Misis Ahmad maza ne, kuma wasunsu sun nuna rashin jin dadinsu game da nasarar da ma'aikaciyar bankin ta samu domin ita mace ce.
Amma wasu mata masu amfanin da shafukan sada zumunta sun shiga muhawarar.
Wata daga cikinsu, Saratu G Abdul, ta yi tsokacin cewar ya kamata Misis Ahmed ta kasance abar koyi, tana mai cewa Al'kur'ani ya "hana mata bude jikinsu."
Sai dai a daidai lokacin da magana a kan hotunan suka fara jan hankali a shafukan sada zumunta, sai aka soma sukar masu tsattsauran ra'yin addini.
Gimba Kakanda, wani marubuci a Najeriya, yana daya daga cikin wadanda suka kare ma'aikaciyar bankin.

Da yake magana da BBC, ya ce masu sukar sun wuce gona da iri.
Marubucin da wasu masu irin ra'ayinsa sun bayyana cewa Najeriya, musamman ma arewacin kasar, tana da wasu matsalolin da suka fi tsanani wadanda ba su da alaka da tufafin mata.

"Abin kunya ne cewa muna muhawara kan kan jiki da kuma tufafin wata mace, yayin da sama da yara miliyan goma a Najeriya ba sa makaranta," in ji Kakanda.
Gimba Kakanda ya kara da cewar: "Ka suranta yaya lamarin zai kasance idan da mun bayar da irin himma da fusatar da muka yi wajen bakanta Misis Ahmad kan warware talauci mai tsanani da karancin ilimi da cin hanci da rashawa a siyasa da kuma ababen more rayuwa da suka baci.".
A halin yanzu Misis Ahmad za ta je zauren majalisar dattawan Najeriya domin a tabbatar da ita a kan wannan mukami.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: