Labarai

Nigeria: Malamai sun fadi jarrabawar ‘yan aji hudu a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na shirin sallamar malamai 21,780 daga cikin 33,000, sakamkon faduwa jarrabawar da aka shirya musu ta matakin ‘yan aji hudu don jarraba kwazonsu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa a yanzu haka jihar Kaduna na neman sababbin malamai guda 25,000, a wani bangaren na shirye-shiryan da take yi don dawo da martabar ilimi a jihar.
Gwamnan jihar Nasir el-Rufai ya gabatar da wannan shirin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Bankin Duniya a Kaduna a ranar Litinin.
”Mun jarraba malaman firamare guda 33,000, mun ba su jabawar aji hudu kuma mu ka ce sai sun samu a kalla kashi 75 bisa 100, amma saidai ina bakin ciki cewa malamai kashi 66 bisa 100 sun fadi.
”A da, an yi amfani da siyasa wajen daukar malamai aiki, amma muna da niyyar sauya hakan ne ta hanyar kawo malaman faramari matasa kuma wadanda suka cancanta, don dawo da martabar ilimi a jihar,” a cewar gwamnan.

Malam el-Rufa’i ya jaddada cewa za a tura malamai wurare daban-daban a fadin jihar don daidaita yawan dalibai da malamai.
Gwamnan ya ce dukkan daraktocin gwamnatin jihar za su mayar da ‘ya’yansu makarantun gwamnati daga shekara mai zuwa, a wani kokari na ganin an inganta tsarin ilimi.
Jami’in Bankin Duniya, Kunle Adekola, ya nuna godiya ga jihar kan yadda take zuba jari a bangaren ilimi da kuma fifiko da ake bai wa yara mata.
Ya kuma ce Bankin zai zuba jari na kimanin miliyan 30 a makarantar firamari ta Rigasa, wadda ta ke da yawan dalibai 22,000, a matsayin wani bangare na goyon bayan kokarin jihar.
NAN ya ruwaito cewa, Shirin Tallafawa Illimi na Bankin Duniya na taimakawa kusan jihohin arewacin kasar 13.
Harkar ilimi a NAjeriya al’amari ne da aka dade ana kokawa kan tabarbarewarsa, musamman ma a arewacin kasar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button