Sports

Neymar ya taya Messi murnar zuwa Rasha

Neymar na Brazil ya fito ya bayyana farin cikinsa akan nasarar da Argentina ta samu na zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a badi a Rasha.

Neymar ya ce ya yi farin-ciki ne saboda abokinsa Messi, wanda ya ci dukkanin kwallaye uku da Argentina ta doke Ecuador, kuma nasarar da ta ba kasar damar zuwa Rasha a badi.

Brazil ma ta taimakawa Argentina a jiya bayan ta doke Chile ci 3-0.

Neymar ya ce duk da cewa yana da abokanai a Chile amma ya zama dole su taka leda domin abin da suka sa gaba shi lashe dukkanin wasaninsu.

Kwallayen da Messi ya ci a jiya ya ja hankali a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ta cewa Argentina ta dogara da dan wasan ne domin tsallakar da ita zuwa Rasha.

Da farko Ecuador ta razana Argentina inda da soma wasa cikin dakika 40 suka jefa kwallo a raga. Daga bisani ne kuma kafin minti 20 Messi ya farke kwallo tare da sake jefa wasu guda biyu.

Nasarar da Messi ya samu na zuwa ne bayan fargabar ko ba zai je Rasha ba, haka kuma ya jagoranci Argentina ga nasara a daidai lokacin da abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo ya jagoranci Portugal ga nasarar zuwa Rasha a badi bayan doke Switzerland.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button