Thursday, 26 October 2017
Nasiha Zuwa Ga ‘Yan Gani Kashe Ni Buhari -Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

Home Nasiha Zuwa Ga ‘Yan Gani Kashe Ni Buhari -Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Ku Tura A Social Media

Assalamu Alaikum
Annabi-tsira da ammincin Allah sutabbata agareshi yace: “Addini nasiha ne. Sai muka ce: ga wa Ya manzon Allah? Sai yace: zuwa ga Allah da Kuma zuwa ga littafinSa da Kuma zuwa ga manzonSa da Kuma zuwa ga shugabanin Musulmi da talakkawansu”.

In kun lura da lafazin Manzon Allah -alaihis salam- a karshen cewa yayi: ” da Kuma zuwa ga shugabanin Musulmi da talakkawansu” ba cewa yayi: ” da Kuma zuwa ga shugabanin Musulmi da Kuma zuwa talakkawansu” ba. Watau Sai Ya dunkulesu gaba daya da nasiha. Wannan fasahar Magana wadda tana daga cikin muijizojin Annabi ta kunshi halin yiwa shugabannin Musulmi da talakkawansu nasiha gaba dayansu ko dai-dai kunsu. Duka sunna ne.
Nashihar da na yiwa Gen. Buhari na kacewansa daya daga cikin shugabanin Musulmi tare da mabiyansa gaba daya ne karkashin Wannan hadisi.

Amma yanzu, a Wannan nasihar na kebe daga cikin mabiyansa ‘yan gamu a kashe ne kawai.
Daga farko in kiransu da suji tsoron Allah da ranar da zaa tadasu ranar tashin alkiyama. Ranar da kowace rai cewa takeyi: “Raina Raina ni kadai”. A ranar za a barka sai kai sai ayyukanka na kwarai da muyagu. A ranar da Shima Gen. Buhari zai tashi Yana cewa: “Raina Raina Ya Ubangijina” A ranar da Allah zai masa hisabi game da ayyunkansa na ibadarsa da Kuma shugabancinsa na Jinin mutane da dukiyarsu da addininsu da sauran hakkokin mutane da kekan shugabanni.

A wancan karon na mulkinsa na farko akwai malaman da suka yi mishi nasiha game da yadda Ya tafiyar da mulkinsa domin shine wajibin malami ba tare da Jin tsoron kowaba sai Allah.
To a yanzu kai ka fito kana zage zage da habaici da bacin rai domin an yi masa nasihar da tafi mashi alheri duniya da lahirassa domin wani kwadayin duniya da kake neman wanda zai ceceka daga azabar Allah ta duniya domin sabonka zuwa ga Allah da fasikancika, ka mance da shi Allah Har kana zagin malami domin baida irin raayinka.  To kayi sauri ka tuba zuwa ga Allah ka nemi afuwar duk wanda ka cutar.
Dalilin yin Wannan nasihar kuwa shine ku ‘yan Gani kashe ni  – kun gurbata akidarku da tawwakkali akan mahaluki ba akan Allan da Ya mallaki komeba. Allah Yace:

Surah Al-Anaam, Ayah ta 17:
(kuma Idan Allah Ya shafeka da wata cuta to babu mai kwaranyewa gareta sai Shi)
Wallahi indan kayi imanin cewa musibar da muka fada cikinta babu mai gyarata sai Buhari kayi shirka. Shin in kura tana maganin zawo tayima kanta mana. Baku ganin yadda Shi kanshi Buhari ya kasa ba kansa mulkin kasan nan domin mulki na Allah ne Har kace : Sai Buhari!
Kuna son ku halaka kank ku halakashi. Kusa masa gururi azucciyarsa. Bawan Allan nan Ya fito yace: Na gaji bazan sake menan shugabancin Kasarnan ba. Amma domin fitinarku kunsa Shi ya fito gaban jamaa ya karyata kansa ya nuna MA jamaa cewa shugabannin musulmi da aka sanu da gaskiya da rike Amana basu da banbanci yanzu da masu yin karya domin neman mulki.

Kuma kun fito Kuna zagin Mai mishi nasiha domin kare maslaha ta alumma da tashi.
Mai makon kubarshi a nuna masa yadda zaiyi kaffaran kurakuransa na baya wanda suna daga cikin sababin jefamu cikin wannan musiba Sai gashi kun fito Yan kanzagi kuna son ku hanashi istigfari domin Sai wanda yayi ikirari dayiwa Allah laifi yake neman gafarassa da menam afwa ga mutanen da yaci zarafin su ya wulakantasu da ukuba Bata shariar Allah ba.
Juyin mulkin da suka yi ba sabo bane Kwai wurrin dokar kasa Kai sabo NE ga Allah. Tunda anyi kuskure kaffarassa shine ya tabbata yaga an dawo da wanda zai hada kan kasa domin shi ne awla. Watau matukar babu kwanciyar hankali babu mulki balle adalci. Kuduba yadda kasahen musulmi suka fada cikin musibu.  Kamar Iraqi da siriya da libiya da Egypt da Somali da yamen. Shin haka kuke son Nigeria tazama?

To haka akeso a wargazamu. Kamar yadda akayi anfani da Boko Haram aka halaka kasar borno haka akeso ayi anfani daku a wargaza mu mu dake yamma. Kunga DE Boko Haram sunfiku ikirari Mai manufa do min su sun labe da sunan Allah ne da sunnan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa.   Amma ku Yan gani akashen mutunne. To wallahi kuyi hattara. Zaazo ayi anfani da ku Bayan an harzukaku a maida ku Kamar Yan taadah Yan Boko Haram masu tada fitina masu tada zaune tsaye.

Ina kiranku da ku sa hankali da natsuwa da basira kukai zucciya nesa Kuma kada kuyi mamakin malamin da adalarsa bata gushe ba in yace kuyi wani abu game da siyasar wannan kasar. Wallahi tallahi ba kusan duk abinda ke kasa ba. Kuma ita siyasa asalinta ta malamai ce ba jahilai ba. Sune ahl aqdi Wal halli. Sune Allah yaba hurumin zaban wanda suka dace da lura da zarafi. Ba Yan banga ba da Yan gamu akashen. Saboda haka musake Jin jahilin da zai hana malamai sa bakinsu acikin harakar siyasa.
Saboda haka kada kayadda kayi fada ko zagi ko kisa domin Buhari ko wani Dan siyasa. Zagin musulmi fasikanci ne Kuma yakinsa kafircine.  Kuma duk wanda ya yi kisa ko yafito aka kashe shi domin siyasar wani mutum ya halaka a wutar jahannama -Allah Ya kare mu daga ita.
Allah Ya shiryar damu Ya hada kanmu zuwa ga alheri da abinda Ya keso. Kuma Ya nisantar damu daga dukkan fitinar karshen zamani. Amin. WA sallallahu ‘Ala nabiyina Muhammad wa ‘Ala Alihi wa sahbihi wa sallam.

Daga Daily Nigerian Hausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: