Friday, 6 October 2017
NAJERIYA Malaman Makaranta Fiye da 500 Aka Kashe Sanadiyar Rikicin Boko Haram a Jihar Borno

Home NAJERIYA Malaman Makaranta Fiye da 500 Aka Kashe Sanadiyar Rikicin Boko Haram a Jihar Borno
Ku Tura A Social Media
Yayin bikin ranar malaman makaranta ta duniya da aka yi a jihar Borno gwamnatin jihar ta sanar cewa tayi hasarar malamanta fiye da dari biyar a shekaru shidan da aka yi ana fama da rikicin Boko Haram
Yayinda ake bikin “Ranar Malaman Makaranta ta Duniya” jiya 5 ga watan Oktoba, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ta kowace shekara don tunawa da karrama malamai, gwamnatin jihar Borno a Nigeria tayi kira akan kungiyoyi masu zaman kansu da su ci gaba da dafawa harkokin ilimi a jihar da yanzu haka ke tangarari sakamakon illar da Boko Haram ta yiwa sha’anin ilimi a jihar, abinda ya janyo mutuwar malamai fiye da 500 da aka kashe.
A cewar mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Usman Durkwa, gwamnatin jihar ta dukufa wajen inganta harkokin ilimin zamani a jihar tare da biyan bukatun malamanta duk da matsalolin
da jihar ke fuskanta.

Alhaji Durkwa ya tunashe da jama’a irin matsalolin da kungiyar Boko Haram ta haifarwa jihar ta fannin ilimi inda har ya kusa durkushewa baki daya. Sai dai yace gwamnatin jihar ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen inganta ilimi.
Gwamnatin jihar ta dukufa wajen gyaran duk makarantun jihar da suka lalace musamman wadanda aka sake kwatowa daga hannun ‘yan Boko Haram a wuraren da suka mamaye a da can.

Shi ma kwamishanan ilimin jihar, Musa Inuwa Kufo ya sanar cewa gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya saki kudin biyan hukumomin jarabawar kare karatun sakandare irinsu WAEC da NECO domin a sakowa daliban da suka kammala karatunsu sakamakon jarabawar da suka dauka.

Shugaban kungiyar Malaman jihar ya bayyana farin cikinsu tare da kuma abubuwan da suke ci masu tuwo a kwarya, inda ya bada misali da rashin biyansu kudin karin girma da na alawus alawus da kuma samar musu ingantattun kayan aiki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: