Thursday, 12 October 2017
Me Ya Sa Ba Za A Kira DAN FIM Da SHEIKH Ba?

Home Me Ya Sa Ba Za A Kira DAN FIM Da SHEIKH Ba?
Ku Tura A Social Media


A wata tattaunawa da Aminu Shariff Momo yayi da mai bayar da umarni  Isah Abubakar Alolo da ya yi fice da lakabin Sheikh a gidan Talabijin na Arewa 24 ya tambaye shi,

Momo: Me ya sa ake kiran ka da Sheikh?

Alolo: Me ya sa ba za a kira ni da Sheikh ba?

Momo: Akasari idan an ce Sheikh za ka ga suna ne na Malaman addini?

Alolo: Fada min su Malaman addinin wa aka yanka rago aka ce sunan sa Sheikh?

Momo: Saboda suna yi wa addini hidima?

Alolo: Ai kowane Musulmi yana yi wa addini hidima, yanzu ko dutse ka gani a hanya ka dauke ka jefar ai aikin lada ne.

Daga kannywoodscence

Share this


Author: verified_user

0 Comments: