Thursday, 19 October 2017
Mata Uku Sun Karbi Musulunci A Garin Tilden Fulani

Home Mata Uku Sun Karbi Musulunci A Garin Tilden Fulani
Ku Tura A Social Media

Daga Ibrahim Bangis Tilde

A yau Laraba (18/10/2017), an samu wasu mata guda uku da suka musulunta a cikin garin Tilden Fulani dake karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Bayan sun musulunta an sauya musu suna kamar haka;

1. Maryam, a da sunanta Monica.
2. Khadija, a da sunanta Blessing.
3. Hafsa, wacce ta ke karamar yarinya ce, ita ma a da sunanta Nancy.

An gudanar da wannan aikin lankwanta masu kalmar shahada ne karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Malamai na reshen Tilden Fulani, Mal Abdullahi Adam tare da rakiyar wasu fitattun mutane a cikin garin Tilde.

Ku na iya ganin wadannan mata yayin da su ka karbi shahada yau a gidan Garkuwan Yamini Alh Aliyu Tasshaqu.

Allah ya tabbatar da dugaduganmu a cikin addinin Musulunci, amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: