Tuesday, 24 October 2017
Labari cikin Hotuna Tsoffin 'Yan Fim Da Na Yanzu Sun Taya Fati Muhammad Murnar Matsayin Da Aka Ba Ta A Gidauniyar Atiku Abubakar

Home Labari cikin Hotuna Tsoffin 'Yan Fim Da Na Yanzu Sun Taya Fati Muhammad Murnar Matsayin Da Aka Ba Ta A Gidauniyar Atiku Abubakar
Ku Tura A Social Media
Daga Aliyu Ahmad
Tsoffin 'yan fim din Hausa na da da na yanzu tare da dimbin masoya da abokan arziki ne suka halarci gagarumar walimar da tsohuwar jarumar finafinan Hausa Fati Muhammad ta shirya domin nuna farin cikin ta kan matsayin da aka ba ta a gidauniyar Atiku Abubakar.
Taron wanda aka gudanar a ranar Juma'ar da ta gabata a Aso Motel dake Waf Road a cikin garin Kaduna, Fati ta shirya shi ne saboda nuna farin cikin ta kan karin matsayin da aka yi mata a gidauniyar, inda a yanzu ita ce Daraktar Mata ta Gidauniyar shiyyar jihohin Arewa Maso Yamma.
A baya dai Fati tana rike da mukamin daraktar mata na jihar Kaduna ne, amma kasancewar rawar ganin da take takawa a tafiyar ya sanya aka yi mata wannan karin matsayi.
Baya ga shugabannin gidauniyar da sauran manyan baki daga sassa daban daban na kasar nan da suka halarci taron, wasu daga cikin sabbi da tsoffin 'yan fim da suka halarci taron, sun hada da Abida Muhammad, Wasila Isma'il, Sadiya Gyale, Hauwa Waraka, Fati Yola, Fati KK, Rahma Sirace, Fati Washa, Sakna Gadaz, Hajiya Binta Kofar Soro, Hadiza Kabara da sauransu.
Sai kuma a bangaren maza akwai, Rabi'u Rikadawa, Adam A. Zango, Tahir I. Tahir, Abbas Sadik, Jamilu Adamu Kocila, Nasir Koki, shugaban hukumar tace finafinai Hausa, Isma'il Na'Abba Afakallah da sauransu da dama.

Ga hotunan kamar hakaShare this


Author: verified_user

0 Comments: