Thursday, 5 October 2017
Kannywood :- Fitattun Fina-finai Hausa 5 da ya kamata ku kalla

Home Kannywood :- Fitattun Fina-finai Hausa 5 da ya kamata ku kalla
Ku Tura A Social Media
Masana’antar kannywood ta shirya damawa da sauran masana’anta shirya fim.
Tun farko shekara ake sako sabbin fina-finai mai dauke da sabon labari kuma mai fadarkawa, ilimantarwa kuma mai koya darasi.

Ga wasu shirin fim 5 da ya kamata ace kun kalla.
An shirya su ne da fitattun jarumai wadanda suka kware a harkar kuma tsare-tsaren da aka bi wajen fitar dasu yana da yawa.

Jaruman sun taka rawa sosai a cikin shirin hakazalika masu wadanda suka shirya su tare da masu bada umarni sun nuna kwarewar su wajen fitar da fina-finan.
Suma marubutan sun taimaka da basirar su wajen rubuta fina-finan.
Ga fina-finan kamar haka;

1.RARIYA
Jaruma Rahama Sadau ta dauki nauyin fitar da wannan shirin kuma Yaseen Auwal ya bada umarni.


2. Kalan dangi
Ita ma jaruma Aisha Aliyu Tsamiya ta shigo sahun sauran jarumai masu daukan nauyin shirin fim. Shirin wanda Ali Gumzak ya bada umarni ya samu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Aminu Sheriff Momo, Hafsat Idris da sauran su.


3. Mansoor
Hakika kowa yaba wannan shiri wanda sabuwar tauraruwar fim Maryam Yahaya tare da Mawaki Umar M.Sheriff suka haska a ciki. Jarumi mai kwazo Ali Nuhu ya bada umarni a shirin.4. Rumana
Kamfanin hikima multimedia ta dauki nauyin fitar da wannan shirin wanda Rahama Sadau, Adam A.Zango, Aminu Sheriff Momo suka taka rawa a cikin ta. Ali Gumzak ya bada umarni.


5. Kujerar wuta
Dalilin da zaka so ka kalli wannan shirin shine akwai tsohuwar tauraruwa Hauwa Maina a ciki kuma ta nuna kwarerta a harkar fim. Halilu umar ya dauki nauyin shirin,bada umurni Faisal Abubakar oyoyo
Kuna iya zuwa kallon su a sinima ko ku tuntubi yan kasuwa domin samun su.

Fim:- Download Mansoor 1&2 , 3& 4 Complete Fim 2017  
Video:- Download KANINA Trailer Film  
Video:- Download KALAN DANGI Trailer Fim

Ku kasance da hausaloaded.com a koda yaushe

Share this


Author: verified_user

0 Comments: