Wednesday, 25 October 2017
Jaruma Daso ta bayyana babban dalilin da ya jefa ta harkar fim

Home Jaruma Daso ta bayyana babban dalilin da ya jefa ta harkar fim
Ku Tura A Social Media


Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood mai suna Saratu Gidado da kuma aka fi sani da sunan Daso ta fito ta bayyanawa duniya babban musabbabin da ya sanya ta shiga harkar fim.

Jarumar da tayi wannan karin hasken a yayin wata fira da tayi da manema labarai a gidan ta dake a birnin Kano dake zaman babbar cibiyar shirya-fina-finan na Hausa.


Hausaloaded.com ta samu dai cewa jarumar a cikin tattaunawar da majiyar mu ta bayyana cewa ita babban abun da ya sa ta shiga harkar fim ka'in da na'in shine saboda ta ilmantar da daukacin al'ummar dake kasar nan musamman ma Hausawa da fulani.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai jarumar ta bayyana cewa ita bata ga banbancin mace mai fita aiki ba alhalin tana da aure da kuma macen auren dake fita yin sana'ar fim inda ta bayyana su a matsayin daya.

Naij. Com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: