Saturday, 28 October 2017
Jami'ar Danfodiyo Ta Sake Samar Da MaCe A Matsayin Farfesa Ta Biyu A sokoto

Home Jami'ar Danfodiyo Ta Sake Samar Da MaCe A Matsayin Farfesa Ta Biyu A sokoto
Ku Tura A Social Media

DAGA MUKHTAR HALIRU TAMBUWAL SOKOTO

Jihar Sokoto ta kai ga Farfesa  mace wadda kuma ita ce mace  ta biyu a jihar a matsayin mace farsesoshi.

Farfesa  Sa'adiyya Omar wadda ta yi karatunta na furamari a Dandago da ke Kano a shekarar 1960 zuwa 1964, ta kuma yi makarantar gaba ga furamari a makarantar 'yan mata ta shekara a 1964-67, sai makarantar "yan mata ta Gwamnati dake Dala, Kano a 1967-1972.

Sannan ta yi digirin farko a fannin ilimin koyarwa na Hausa a jamiar Bayero a 1977. Ta yi hidimar kasa 1977-78, sannan ta yi digiri na biyu a fannin Hausa a jami'ar SOAS da ke Landan a 1984, sai digirin digirgin a jami'ar Danfodiyo ta Sokoto a 2010.

Farfesa Sa'adiyya Omar, ta rike wasu mukamai a jami'ar Usmanu dan Fodiyo da suka hada da: Daraktan Cibiyar Nazarin Hausa  a 2013-17, mamba a kwamitin zartarwa na jami'ar, da sauransu, ta kuma yi zama a wasu kwamitocin da suka hada Shugabantar kwamitin Amintattu na musabakar Al-kur'ani Mai girma ta kasa Wadda jami'ar take shiryar daga shekarar 2013 Zuwa yau, kwamitin kula da Gidajen Dalibbai, kwamitin shiryar jarabawar Dalibbai, Kwamitin shirya bikin Yaye dalibban jami'a, da sauran kwamitoci.

Haka kuma ta bada gudunmawa cikin wasu kwamitoci daban daban wadan da ba na cikin jami'ar ba da suka hada da :Kwamitin bincike kan cin zarafin yara a manyan makarantun, na kwalejin ilimi ta tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara., Wasu kwamitoci a makarantinnen Yan mata ta Nana, da ke Sokoto, Ta Sarkin Musulmi Bello ta ke Sokoto, Tana cikin Kwamitin da Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa dan Kula da Gidan marayu mallakar jihar, kwamitin lamurran mata a matakin kasa da ke legos a shekarar 1991, Mamba a kwamitin Amintattu na hukumar mata ta jihar Sokoto a shekarar 1991.

Shehiyar malamar ta Tayiwa Addini da Al-ummah hidimomi a wurare Dabandaban da suka hada da : Shugabar kungiyoyin Tarayyar mata musulmi ta kasa (Fomwan)  a shekarar 1993 zuwa 1997,Amirar Fomwan reshen jihar Sokoto a 1985 zuwa 1992, Amirar Kungiyar  Mata musulmi (MSO)  reshen Jihar Sokoto a shekarar 1997 zuwa 2000,Jni da sauran su.

Farfesar, ta yi dinbin rubuce rubuce da makaloli masu yawan Gaske da suka hada da : Rubuta Littafin Fasahar Mazan Jiya, wanda ke Nazari akan Rayuwa da Wakokin Malam Mu'azu Hadeja, Littafin Modibbo Kilo ( Diya ce ga Nana Asmau Yar Shehu Usmanu bn Fodiyo) Mai bayanin Rayuwar ta da Ayukkanta. Wani  littafin da ta rubuta shine :Yan taron Nana Asmau diyar Dan Fodiyo .(Dalibban ta) Mai bayani a kan Tasirin da Taskance Wakokin Su. Tare da littafin Malammai Mata na Daular Usmaniyya a karni na 19 da 20.
Akwai sauran littafai da ta rubuta da wasu da ke tafe da wadanda take akan rubutawa tare da dinbin mukaloli daban daban da ta gabatar ciki da wajen kasar nan.

Farfesa Saadiyya, ta yi tafiye tafiye a wasu kasashe da suka hada da : Saudiyya, Ingila, Masar, Sudan, Nijar, Athens-Greece, Astoria, Malaysia, China da sauran su.

Farfesa tana da Yara biyar da jikoki da dama, Margayi Dr. Omar Bello Dan masarautar sokoto kuma jinin Shehu Usmanu Dan Fodiyo shine baban yaran na ta.

Muna yiwa farfesa fatar Alheri da samun Nasarori a rayuwar ta da Gamawa lafiya.  Amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: