Tuesday, 3 October 2017
Hukumar Zaben Najeriya Zata Dawo Da Rajista a Matakin Gunduma

Home Hukumar Zaben Najeriya Zata Dawo Da Rajista a Matakin Gunduma
Ku Tura A Social Media
WASHINGTON DC — Hukumar Zaben Najeriya ta ce ta riga ta yi nisa wajen kamala shirye shiryen Zaben shekara 2019.

Shugaban Hukumar Zaben Farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya baiyana haka a wata hira ta mussamman da Wakiliyar Sashin Hausa Medina Dauda a Abuja.
Farfesa Mahmood ya ce hukumar Zaben ta na cigaba da yin rajistan masu zabe domin yiwa wadanda basu samu yin rajista a baya ba da kuma wadanda yanzu shuka cika shekaru goma sha takwas.

Ya kara da cewa a shekarar mai zuwa hukumar zata dawo da rajistan matakin gunduma wanda kuma a yanzu haka akwai gundumomi 8,809, a fadin Najeriya, kuma yin haka zai taimaka sosai. Ya cigaba da cewa daga lokaci da hukumar ta fara rajistan masu zabe a cikin watan Afrilun, bara zuwa yanzu an yi rajistan ‘yan Najeriya, miliyan biyu da dubu dari bakwai.

Shugaban hukumar yana da yakinin cewa idan har aka cigaba da yin rajistan har zuwa kwana sittin kafi lokacin babban zaben ,mai zuwa kamar yadda doka ta tanada za a iya yiwa sauran ‘yan Najeriya da suka rage.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: