Saturday, 7 October 2017
Gwamnonin Arewa Kuna Ba Ni Tsoro, Inji Sheikh Sani Jingir

Home Gwamnonin Arewa Kuna Ba Ni Tsoro, Inji Sheikh Sani Jingir
Ku Tura A Social Media
Daga Comrade Salim Abubakar Imam Jingir

Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'ikamatus Sunnah yayi kira ga gwamnonin arewa da suka kasa biyan albashi da su ji tsoron Allah su biya.

Sheikh Jingir ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da nasiha a masallacin Juma'a na 'Yan Taya dake cikin garin Jos, ya kuma kara da cewa "a gaskiya ya kamata gwamnonin mu Arewa ku dinga karasa aikace-aikacen gwamnonin da kuke gada, saboda ta haka ne Arewa za ta cigaba".

Sheikh Jingir ya kuma yabawa gwamnonin da suka mulki jihar Legas wajen kokarin karasa aikace-aikacen da suka gada daga gwamnonin baya. Daga karshe sheikh ya yi addu'a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan Allah ya kara masa lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: