Tuesday, 3 October 2017
Fati Mohammed Ta Zama Daraktar Mata Na Gidauniyar Atiku Reshen Arewa Maso Yamma

Home Fati Mohammed Ta Zama Daraktar Mata Na Gidauniyar Atiku Reshen Arewa Maso Yamma
Ku Tura A Social Media
Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Hajiya Fati Muhammad ta samu karin matsayi a gidauniyar Atiku Abubakar, inda yanzu ta samu matsayin daraktar mata na gidauniyar a shiyyar arewa maso yamma.

 Kafin wannan matsayi Fati ita ce daraktar mata na gudauniyar reshen jihar Kaduna.

Jihohin da Fati za ta jagoranta sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Jigawa da Zamfara.

Gidauniyar ta Atiku ta kasance tana tallafawa marasa karfi, wadanda suka hada da talakawa, marayu, 'yan gudun hijira da sauransu.
Ga hotunan domin gasgatawa:-

Share this


Author: verified_user

0 Comments: