Sunday, 22 October 2017
Duniya Ina Zaki Da Mu:- Ta baiwa yar'uwar ta kwaya mai bugarwa kana ta sa saurayinta yayi mata fyade !!!

Home Duniya Ina Zaki Da Mu:- Ta baiwa yar'uwar ta kwaya mai bugarwa kana ta sa saurayinta yayi mata fyade !!!
Ku Tura A Social Media
Hausawa na cewa yan uwa rabin jiki ne su shin ko wannan kalamai zasu samu wuri a wannan labarin?, Ta yaya mace zata baiwa yar uwar ta kwaya mai bugarwa kana ta ba saurayin ta damar yin fyade da ita?
Shugaban wani kungiyar kare yancin dan adam Prince Harrison Gwamnishu ya gano wata matashiya mai shekaru 17 da yar uwar ta baiwa kwaya mai bugarwa kana ta sa saurayinta yayi mata fyade har ma ta samu ciki.

Prince Gwamnishu ya daukaka kara bayan matashiyar ta zargi yar uwar ta da saurayinta da hada gwiwa wajen yi mata fyade har ma ta samu ciki.
ga labarin kamar yadda ya rubuta
"Ogechukwu ta taho jihar Legas inda take zama da yar uwar ta dake nan yankin Ojo . Yar uwar tana sana'ar siyar da kayan sawa kuma a boye tana kai ma mazaje dake yankin mata domin suyi lalata dasu.

Yar uwar ta sha neman sanya Ogechukwu a sana'ar da take amma ta ki amincewa domin tana alfahari da budurcin ta.
Cikin watan Afrilu na bara Ogechukwu ta sha lemun wanda yar uwar ta bata yayin da take bikin zagoyowar ranar haihuwar ta. Ba da sanin ta ba ashe an sanya kwaya mai sanya mutum yayi bacci a cikin lemun.

Washe garin da ta farka sai ta gan jini na malala a farjin tare da yaruwar da saurayin a bakin inda take kwance. Sai yar'uwar tace mata ai babu laifi idan ta rabu da budurcin ta.
Da jin haka cikin fushi Ogechukwu ta bar gidan ta koma ma dan uwan ta dake garin Asaba nan jihar Delta inda ta kora masa labarin abun da ya same ta a wajen yar'uwar ta dake Legas.

Bayan yan satutuka Ogechukwu ta gano cewa tana da juna biyu. Da hakan ta fara aikin koyarwa domin taimakon kanta. Ranar alhamis 12 ga watan octoba ne wanda ya dauke ta aiki ya kulle ta tare da wasu guda biyu bisa ga zargin satar naira dubu sittin (N60,000).
Sauran mutanen sun samu damar yin beli amma ita bata samu ba domin bata kudin yin haka.
Shugaban kungiyar kare yancin dan adam na behind bars innitiative ya ziyarci gidan yari da aka kulle ta har suka ci karo inda ta kora mai labarin abun da ya faru da ita.
Bayan haka ya taimaka wajen fitar da ita daga gidan yarin har ma ya kara da cewa ita da dan uwanta zasu taho Legas domin kai karar yar uwar da saurayin da suka zama silar halin takaici da take ciki.

Share this


Author: verified_user

0 comments: