Darakta Ya Rataye Kansa A Jihar Kogi Saboda Rashin Biyan Albashi Na Watanni Sha Daya

Wani darakta a jihar Kogi mai suna  Edward Soje ya rataye kan sa a jikin wata bishiya saboda rashin karbar albashi na kusan watanni sha daya.

Daraktan dai ya hallaka kansa ne kwanaki goma bayan matar sa ta haifa masa 'yan uku a wani asibiti mai zaman kan sa dake Abuja.

Soje ya rataye kansa ne a lokacin da ya ziyarci matar sa a Abuja, inda ya bar mata wasikar ban kwana, yana yi mata nasiha cewar Allah zai kula da ita da jirajiran ta guda uku.

 Daga Sani Twoeffect Yawuri

Share this


0 comments:

Post a Comment